MƊD ta buƙaci gudanar da bincike kan kisan fararen hula sama da 100 a Burkina Faso

0
156

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi ƙiran da a gudanar da bincike mai zaman kansa kan “kashe-kashen da aka yi a Burkina Faso cikin wannan watan, da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama, ciki har da ƙananan yara.

Mai shigar da ƙara na gwamnatin Burkina Faso, a ranar litinin da ta gabata ya ce sama da mutane 70 ne aka kashe yayin wani hari da aka kai Zaongo da ke tsakiyar arewacin ƙasar a ranar 5 ga watan Nuwamba, kuma yawancinsu yara ne da kuma tsofaffi.

Ofishin kare hakkin bil adama na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce yana “bin diddigin munanan rahotannin kashe-kashen da aka samu a ƙasar da ke yammacin Afirka.

“Muna ƙira ga gwamnatin rikon kwarya da su gudanar da cikakken bincike, mai zaman kansa, da kuma gaskiya kan waɗannan rahotanni masu tada hankali,” in ji mai magana da yawun Liz Throssell a cikin wata sanarwa.

Jami’ar ta ce mahukunta sun tabbatar da mutuwar mutane aƙalla 70, amma wasu rahotanni sun nuna cewa adadin waɗanda aka kashe sun haura 100, inda wasu da dama jikkata”.

KU KUMA KARANTA: Tallafin abinci na ‘yan gudun hijirar Sudan a Chadi yana dab da ƙarewa – MƊD

Ƙasar dai na fama da hare-haren daga masu iƙirarin jihadi da ya samu asali daga makwabciyar ƙasar Mali a shekarar 2015 da ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula da sojoji sama da dubu 17 tare da raba mutane miliyan biyu da muhallansu.

Gwamnatin riƙon ƙwaryan soji ke mulkin Burkina Faso tun bayan juyin mulkin da suka yi a watan Satumban 2022.

Leave a Reply