Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce za a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun naira kuma za su ci gaba da kasancewa halastattu har bayan wa’adin 31 ga watan Disamban 2023 da aka sanya.
Wata sanarwa da daraktan sadarwa na CBN, Isa AbdulMumin ya fitar, ta buƙaci ’yan Najeriya su ci gaba da amfani da tsofaffin takardun naira na 200, 500 da kuma 1000 har sai abin da hali ya yi.
Sanawar ta CBN ta kuma umarci bankunan kasuwanci da sauran cibiyoyin hadar-hadar kuɗi da su ci gaba da karɓar tsofaffi da sabbin takardun naira.
Ya bayyana cewa an ɗauki matakin ne daidai da tsarin hada-hadar kuɗi ta ƙasashen duniya da kuma hana faruwa halin matsi da aka shiga a baya.
Sanarwar ta ƙara da cewa bankin CBN yana aiki da sauran hukumomi don ganin an janye ƙarar da kuma soke umarnin kotun da sanya wa’adin na ranar 31 ga watan Disamba.
KU KUMA KARANTA: Za mu janye tsofaffin takardun naira a hankali – CBN
A watan Oktoban 2022 ne tsohon Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya jagoranci ƙaddamar da tsarin sauya fasalin takardar naira na 200, 500, da kuma 1000, kuma ya ba da wa’adin dakatar da karɓar tsoffin takardun kuɗin.
Matakin na Emefiele ya zo ne gab da babban zaɓen 2023, wanda da ya jawo zargin gwamnan bankin ya yi hakan ne domin kayar da jam’iyyar APC mai mulki, bayan ya faɗi zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwarta.
Dambarwar sauyin kuɗin da kuma takaita cirar tsabar kuɗi a lokacin ya jefa ’yan Najeriya cikin tashin hankali da matsin rayuwa, wanda haka ya sanya wasu gwamnoni maka shi a kotu suna ƙalubalantar umarnin daina amfani da tsofaffin takardun kuɗin.