Za mu taimaka wa Najeriya ta gyara matatun manta – Saudiyya

0
175

Gwamnatin ƙasar Saudiyya ta yi alkawarin zuba jari domin farfaɗo da matatun man Najeriya da kuma taimaka wa gwamnati ta aiwatar da tsare-tsaren daidaita darajar naira.

Yariman Saudiyya, Muhammad Bin Salman ne ya yi alkawarin yayin tattauna da Shugaban Najeriya, Bola Tinubu a gefen taron ƙasar da ƙasashen Afirka da yake gudana a Riyadh, babban birnin ƙasar.

Saudiyya ta kuma yi alƙawarin tallafa wa Najeriya, ta hannun Babban Bankin Najeriya (CBN), domin a farfaɗo da darajar naira.

KU KUMA KARANTA: Za a yi taron ƙasashen Musulmai da na Larabawa a Saudiyya kan yaƙin Gaza

Yarima Muhammad, a cikin wata sanarwa da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya kuma yabawa manufofin tattalin arzikin da Shugaba Tinubu yake aiwatarwa.

A cewar Yariman na Saudiyya, ƙasar shi ta ƙagu ta ga Najeriya tana bunkasa a ƙarƙashin Shugaba Tinubu, musamman a matsayinta na jagaba a Afirka.

Leave a Reply