Kanada ta rufe ofishin jakadancinta a Nijeriya bayan gobara ta tashi

0
149

Kanada ta dakatar da ayyuka a ofishin jakadancinta da ke Nijeriya har sai yadda hali ya yi, kana ta yi gargaɗi ga ‘ya’yanta kan yawan tafiye-tafiye marasa muhimmanci zuwa ƙasashen yammacin Afirka.

Tuni aka ƙaddamar da bincike bayan tashin gobarar a ofishin jakadancin a ranar Litinin wadda ta yi sanadin mutuwar mutum biyu, a cewar Ministar harkokin wajen ƙasar Melanie Joly.

Jami’an kashe gobara sun ce wani tankin ajiye fetur da ke cikin ginin injin janereto ne ya kama da wuta, inda ma’aikata biyu da ke kula da janaretan suka mutu.

Kazalika mutane biyu sun jikkata sakamakon tashin gobarar.

“Muna tabbatar da cewa an samu fashewar wani abu a babban Ofishin jakadancinmu a Nijeriya, gobara ce ta tashi kuma muna bincike don gano musabbabin abin da ya faru,” in ji Joly a shafinta na X.

Sai dai babban Ofishin bai ce komai ba game da gobarar amma a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X ya ce an “dakatar da ayyukan Ofishin har sai baba ta gani.”

Mai magana da yawun shugaban Nijeriya, Ajuri Ngelale, ya ce an samu asarar rai da waɗanda suka jikkata a gobarar amma bai bayyana adadin mutanen ba, a cewar wata sanarwa da ya fitar.

KU KUMA KARANTA: Babban ofishin jakadancin ƙasar Kanada a Najeriya ya kama da wuta a Abuja

Sharuɗɗa kan tafiye-tafiye

Ofishin jakadancin ya fitar da wasu sharuɗɗa kan tafiye-tafiye, inda ya buƙaci ‘yan ƙasar Kanada su guji yin balaguro mara muhimmanci zuwa Najeriya, ciki har da Abuja babban birnin ƙasar, “saboda yanayin tsaro na rashin tabbas a duk faɗin ƙasar da kuma haɗarin hare-haren ta’addanci da laifuka da rikice-rikicen ƙabilanci da kuma hare-hare da makamai da garkuwa da mutane.”

A ranar Juma’a ne ƙasar Amurka da Birtaniya suka fitar da sanarwar cewa akwai “mummunar barazana ga manyan otal-otal a manyan biranen Nijeriya” tare da gargaɗi kan tafiye-tafiye zuwa ƙasar mafi yawan al’umma a Afirka.

Ƙasashen Yamma da ke da ofisoshin jakadanci a Nijeriya suna yawan fitar da sanarwar gargaɗi kan tafiye-tafiye zuwa ƙasar, lamarin da gwamnati Nijeriya ta sha watsi da sha yin watsi da shi.

Leave a Reply