An kama ‘yan ta’addan da suka tsere daga gidan yari a Tunisia

0
133

Jami’an tsaro a Tunusia sun samu nasarar kama mutane biyar masu tsatsauran ra’ayin addini, da suka gudu daga gidan yarin da ake tsare da su a makon da ya gabata, bisa aikata laifin kashe wasu ‘yan siyasa biyu da kuma ‘yan sanda.

Ma’aikatar kula da harkokin cikin gida ta ƙasar ta ce, da sanyin safiyar talatar nan ce aka kama mutane 4 daga cikinsu a tsuburin da ke kusa da birnin Tunis, sannan cikon na biyar din an kama shi kwanaki biyu da su ka gabata tare da taimakon jama’a.

Tserewar ta su daga gidan yari ya sanya gwamnatin ƙasar ɗaukar matakin korar wasu manyan jami’an sirri, sakamakon sakacin da ake ganin an samu a sha’anin tsaro.

Hukumomin tsaro sun bayyana mutane a matsayin ‘yan ta’adda da ke da hatsari, domin daga cikinsu akwai Ahmed Malki da aka fi sani da Somali, wanda ya ke fuskantar ɗaurin shekaru 24 bisa kashe ‘yan siyasa Chokri Belaid da kuma Mohamed Brahmi a shekarar 2013.

KU KUMA KARANTA: An kama tsohon shugaban mulkin sojan Guinea da ya tsere daga gidan yari

Tun bayan komawa mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 2011 a Tunisia, kungiyoyin masu ikirarin jihadi sun kashe ‘yan sanda da masu yawon shakatawa da dama a kasar, duk da cewar gwamnatin ƙasar ta yi nasarar kashe ko kama wasu manya da ke cikinsu a ‘yan shekarun nan.

Leave a Reply