Fitaccen Malamin addinin Musulunci Sheikh Dokta Yusuf Ali ya rasu

0
151

Allah ya yi wa fitaccen malamin addinin Musulunci a jihar Kano, Sheikh Dokta Yusuf Ali rasuwa.

Sheikh Dokta Yusuf wanda shi ne Sarkin Malaman Gaya ya rasu ne a daren lahadi bayan ’yar gajeriyar rashin lafiya, yana da shekaru 73.

‘Yar marigayin, Dokta Bilkisu Yusuf Ali ta shaidawa Aminiya cewa za a yi janaizarsa a yau Litinin da Azabar a Masallachin Murtala da ke kan titin Gidan Zoo.

Shehin malamin ya gudanar da rayuwarsa ta aikin gwamnati a matsayin alkali, inda ya jagorancin kotunan Shari’ar Musulunci daban-daban a Jihar Kano, kafin ya yi ritaya a shekarar 2009.

Bayan koyarwar addinin da ya ɗauki tsawon lokaci yana yi, malamin ya yi tashe wajen taimaka wa al’umma ta ɓangaren neman lafiya daga shafar aljanu.

Leave a Reply