Chadi ta sanar da janye jakadanta daga Isra’ila

0
145

Ƙasar Chadi ta sanar da yi wa jakadanta da ke Isra’ila ƙiranye sakamakon hare-haren da ƙasar ke kai wa Gaza.

A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Chadi ta fitar a ranar lahadi, ta yi Allah-wadai da irin yadda ake samun asarar rayuka a Gaza tare da ƙira kan a tsagaita wuta. Haka kuma ta yanke shawarar yi wa jakadanta ƙiranye daga Isra’ila zuwa N’Djamena domin tattaunawa.

“Chadi na mayar da hankali sosai kuma ta damu kan abin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya, musamman tashe-tashen hankulan da ba a taba ganin irinsu ba a Zirin Gaza.

“Sakamakon wannan bala’in, Chadi ta yi Allah wadai da rasa rayukan farar hula da dama tare da neman a tsagaita wuta wanda zai kai ga mafita mai ɗorewa ga Falasɗinu,” in ji sanarwar.

KU KUMA KARANTA: Turkiyya ta janye jakadanta daga Isra’ila

“Dangane da haka ne aka yanke hukuncin yin ƙiranye ga jakadan da ke Isra’ila domin tattaunawa,” kamar yadda sanarwar ta ƙara da cewa.

Da alama ce Chadi ƙasar Afirka ta farko da ta soma ɗaukar irin wannan matakin daga nahiyar Afirka, duk da cewa tuni kasar Turkiyya ta ɗauki wannan matakin na yi wa jakadanta ƙiranye.

Haka ma ƙasashen Bolivia da Chile da Colombia da ke Kudancin Amurka tuni suka ɗauki matakin yanke dangantaka da Isra’ilar sakamakon ci gaba da kisan da take yi wa Falasɗinawa.

Zanga-zangar kin-jinin Isra’ilar na ci gaba da kankama a ƙasashe da dama ciki har da Amurka da kuma Birtaniya. Zuwa yanzu akalla Falasɗinawa 9,970 Isra’ila ta kashe a Gaza, daga ciki 4,800 yara ne ƙanana, sannan 2,550 mata ne.

Leave a Reply