Gwamnatin Legas ta ƙwace sama da motoci 100 da suke kwana a kan gadoji

Hukumar Kula da Ababen Hawa ta Jihar Legas (LASTMA) ta ce ta ƙwace motoci sama da 100 da ake ajiye su a kan gadoji.

Motocin da aka kama sun haɗa da na haya da ma waɗanda ba na haya ba.

An yi kamen ne a ƙarshen wa’adin mako ɗaya da gwamnatin Jihar ta ba masu motocin bas-bas da tifofi da ta ce sun mayar da kan gadojin a matsayin wuraren ajiye motoci da na gyaransu.

Mai ba Gwamnan Jihar shawara kan harkokin sufuri, Sola Giwa ne ya jagoranci aikin duba ababen hawan.

KU KUMA KARANTA: Yadda fusatattun matasa suka ƙone mutum biyar da ake zargin ɓarayi ne masu amfani da babur na adaidaita

Ya ce sun ɗauki matakin ne domin tsaftace hanyoyi da kawo ƙarshen yadda ababen hawa suke kawo cunkoso a kan gadojin.

Sola ya ce an ƙwace ababen hawan ne a kan gadojin da ke unguwannin Ejalonibu da Obalende da Apongbon Ebute-Ero, Idumota da ke Jihar.

Hadimin Gwamnan ya ce za su ci gaba da aikin har sai sun tsaftace hanyoyin jihar daga cunkoso kamar yadda gwamnatin Jihar mai ci ta ƙuduri aniyar yin haka.

Sai dai ya ce nan ba da jimawa ba za su gurfanar da dukkan motocin a gaban kotun tafi-da-gidanka ta ababen hawa domin su fuskanci hukunci.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *