An kama waɗanda ake zargi da kashe wata mata, ta hanyar yi mata yankan rago a Gwambe

0
201

Ƙasa da sa’o’i 48 da yi wa wata mata yankan rago a Gwambe, rundunar ’yan sandan jihar ta sanar da cafke wasu daga cikin waɗanda ake zargi da aika-aikar.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar ne ya bayyana hakan a wata taƙaitacciyar sanarwa da ya fitar a Yammacin wannan Lahadin.

Ya ce ababen zargin da suka shiga hannu, nan gaba kaɗan za su gabatar da cikakken bayanin yadda aka kama su da kuma gabatar da su wa manema labarai.

An ruwaito cewa, wasu da ake zargin ’Yan Kalare ne suka yi wa matar mai ’ya’ya takwas yankan rago a garin Gombe.

Bayanai sun ce maharan sun shiga gidan Malama Aishatu Abdullahi mai shekaru 58 ne a daren Juma’a, suka yi mata yankan rago a unguwar Jekadafari.

Wani rahoto da Aminiya ta samu daga hadimin Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya kan sha’anin tsaro da harkokin gwamnati, Ambasada Yusuf Musa Danbayo, ya ce ana kyautata tsamnanin turo su aka yi su kashe matar.

KU KUMA KARANTA: An yi wa mace mai ’ya’ya 8 yankan rago a Gwambe

Ya bayyana cewa maharan sun shiga gidan Malama Aishatu ne da misalin ƙarfe 9 na dare aka yi mata yankan rago sannan suka tsere da wayar salularta.

Hadimin gwamnan ya ce bayan faruwar lamarin an sanar da ’yan sanda kuma nan take suka ziyarci gidan suka ɗauke ta zuwa asibitin ƙwararru na jihar.

Kakakin ’yan sanda na jihar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ya ce a lokacin da jami’ansu suka isa gidan marigayiyar, sun tarar da ita kwance male-male cikin jini, suka ɗauke ta zuwa asibitin inda a nan ne likita ya tabbatar da mutuwar ta.

Tuni dai kwamishinan ’yan sandan jihar, ya ba da umarnin a gagguata fara bincike don gano waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki.

Tun a ranar Juma’ar ya bayyana cewa rundunar ba za ta zauna ta naɗe hannu miyagun abubuwa irin haka na faruwa ba, don haka sai sun zaƙulo waɗanda suka aikata laifin dan fuskantar shari’a

Daga nan sai yace dokar nan da aka sanya ta taƙaita zirga- zirgar jama’a daga ƙarfe 12 na dare tana nan ba canji.

Leave a Reply