Kotun ƙolin Najeriya ta fidda ranar fara shari’ar zaɓen Tinubu da Atiku

0
288

Kotun ƙoli ta sanya ranar Litinin 23 ga watan Oktoba, don fara sauraron ƙarar da Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, babbar mai adawa a Najeriya, ya ɗaukaka a kan zaɓen 2023.

A wata sanarwa da magatakardar kotun Zainab M Garba ta sanya wa hannu, ta zayyana hukumar zaɓe ta INEC da wasu, a matsayin waɗanda ake ƙara.

Atiku Abubakar dai ya yi alƙawarin ɗaukaka ƙara ne a kan hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaɓe na ranar 6 ga watan Satumba da ya tabbatar da nasarar Bola Tinubu.

Jagoran adawar na Najeriya ya samo ƙarin shaida a kan ƙarar da ya shiga yana ƙalubalantar cancantar Tinubu, inda yake fatan Kotun ƙolin za ta ba shi damar gabatar da ita, yayin da take sauraron shari’arsa.

KU KUMA KARANTA: Kotu a Amurka ta umarci jami’ar Chicago ta bai wa Atiku damar ganin takardun karatun Tinubu

Hukumar zaɓe ta INEC ta ayyana cewa Bola Tinubu na jam’iyyar APC ya samu ƙuri’a 8,794,726, yayin da ta ce Atiku Abubakar ya samu ƙuri’a 6,984,520.

Sai dai a ƙarar da ya ɗaukaka gaban Kotun ƙolin, Atiku ya shigar da hujjoji guda 35, waɗanda yake cewa bisa la’akari da su, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa a ƙarƙashin Mai shari’a Haruna Tsammani ta “tafka babban kuskure”.

A takardar ɗaukaka ƙarar da babban lauyan ɗan takarar na PDP, Chris Uche ya shigar, Atiku Abubakar ya roƙi kotun ta jingine duk abubuwan da kotun zaɓen shugaban ƙasa ta gano da kuma matsayar da ta cimma.

Leave a Reply