An kama Lauyan bogi, wanda ya yi nassara a shari’o’i 26 a gaban manyan alƙalai

0
310

Hukumomin ƙasar Kenya sun kama wani lauya na bogi, Brian Mwenda, wanda ya yi nasara a ƙararraki 26 a lokacin da yake gabatar da kansa a matsayin lauyan babbar kotun ƙasar Kenya.

Rahotanni sun ce lauyan ya gudanar da ƙararraki 26 a gaban alƙalan manyan kotuna da alƙalan kotun ɗaukaka ƙara infa ya yi nassara a shari’ar da ya wakilta kafin a kama shi.

Ƙungiyar Lauyoyi ta Kenya (LSK) reshen Nairobi Rapid Action Team (RAT) ta kama shi saboda sha’anin ƙarya, lokacin da suka sami ƙorafin jama’a.

KU KUMA KARANTA: An kama sojojin bogi guda biyar a jihar Legas

Reshen Nairobi ya bayyana a shafinsu na X cewa shi ba lauya ba ne kuma ba shi da lasisin yin aikin lauya a Kenya.

“An gabatar da shi ga LSK Branch Nairobi ta hanyar Ƙungiyar Rapid Action Team (RAT), cewa mutumin ya kasance yana gabatar da kansa a matsayin Lauyan Babban Kotun Kenya kuma memba na LSK Nairobi Branch,”

Leave a Reply