Jami’o’in ƙasashen waje 270 ne suke so mu ba su lasisi a Najeriya – NUC

0
247

Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) ta ce aƙalla jami’o’in ƙasashen waje 270 ne yanzu haka suke neman a ba su lasisin kafa jami’o’i a Najeriya.

Shugaban hukumar na ƙasa, Dakta Chris Maiyaƙi, ne ya bayyana haka yayin wani taron ƙara wa juna sani da Hukumar Raya Al’adun Birtaniya ta shirya a Abuja ranar Alhamis.

Ya kuma ce tuni Gwamnatin Tarayya ta buɗe ƙofarta domin ta ba jami’o’in ƙasashen waje dama su shigo a dama da su a fannin ci gaban ilimi a Najeriya a ƙoƙarinta na inganta fannin.

Dakta Chris ya ce sun ɗauki matakin ne domin ganin karatun jami’o’in Najeriya ya yi kafaɗa da kafaɗa da na kowace ƙasa a duniya, inda ya ce dama haka ya kamata tsarin karatun jami’o’i ya zama.

KU KUMA KARANTA: Jami’ar Isyaku Rabi’u za ta fara karatu a watan Janairu

Shugaban na NUC ya ce, “Duk da jami’o’i sama da 270 ɗin da muke da su a Najeriya, har yanzu muna aikin ganin mun faɗaɗa adadin, yanzu haka ma akwai jami’o’in waje sama da 270 da ke neman a ba su lasisin kafawa a Najeriya.”

Kodayake ya ce akwai tsauraran sharuɗan da dole sai an cika su kafin su ba da lasisin, amma ba zai yiwu su ci gaba da rufe ƙofofinsu ga makarantun ba.

Tun da farko, Daraktan Shirye-shirye na hukumar ta Birtaniya a Najeriya, Chikodi Onyemerela, ya ce an shirya taron ne da nufin ganin an samu alaƙa da haɗin gwiwa tsakanin jami’o’in Najeriya da na Birtaniya domin su yi aiki kafaɗa da kafaɗa.

Leave a Reply