INEC ta musanta janyewa daga ɗaukaka ƙarar Abba kan Gawuna

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, (INEC), ta musanta janye ƙarar da ta shigar a kan ƙarar zaɓen gwamnan Kano da ake yi.

Jaridar Vanguard to rawaito Kwamishinan INEC na ƙasa kuma shugaban kwamitinta kan yaɗa labarai da wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a, Sam Olumekun ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Abuja.

Ya ce jami’in shari’a na hukumar, wanda ake zargin ya janye daga shari’ar, an ɗauki matakin ladabtarwa a kansa.

Ya ce: “An jawo hankalin Hukumar kan rahotannin kafafen yaɗa labarai bisa wata wasiƙa da jami’in shari’a na ofishinmu na Jihar Kano ya rubuta cewa hukumar ta janye daga ƙarar da ta shigar a kan ƙarar da ake yi na zaɓen Gwamnan Kano.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta umarci gwamnatin Kano ta biya diyyar rushe-rushen shagunan ‘yan kasuwa a jihar

“Muna so mu bayyana sarai cewa wasiƙar ba ta da izini.  Tuni dai aka janye shi kuma jami’in yana fuskantar matakin ladabtarwa.

“Don haka ana shawartar jama’a da su yi watsi da zancen janyewar hukumar daga shari’ar”.

“Muna so mu bayyana dalla-dalla cewa inda masu shigar da ƙara suka sa INEC a cikin wani lamarin shari’ar, hukumar tana da haƙƙin ta mayar da martani.

“Saboda haka, mun umurci lauyoyinmu da su ci gaba da bin ƙa’idojin Hukumar.  Manufar ba ta canza ba.”


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *