Da gaske ne an yi yunƙurin juyin mulki a Congo Brazzaville?

0
353

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnatin Jamhuriyar Congo ta musanta labaran da ta ƙira na “Ƙanzon kurege” a kafafen sada zumunta wanda suke cewa an yi Juyin mulki a ƙasar. Wasu labarai marasa tushen sun ce ana shirin gudanar da wani abu a Brazzaville mai kama da juyin mulki.

Gwamnati ta musanta waɗannan labarai. “Muna tabbatarwa da mutane babu wani abun tashin hankali kuma muna ba su shawarar kowa ya koma ya ci gaba da harkokinsa na yau da gobe,” kamar yadda kakakin gwamnati Thierry Moungala ya wallafa a shafinsa na X da a baya aka fi sani da Twitter.

Juyin mulki a yankin Yammacin Afrika na neman zama ruwan dare a ‘yan shekarun nan.

Sojoji ne ke shugabantar ƙasashen Mali da Burkina Faso da Guinea da Nijar da kuma Gabon, suna kafa hujja da cewa shugabannin da suka hamɓarar sun gaza kawo ƙarshen matsalar tsaro musamman a ƙasashen yankin Sahel.

KU KUMA KARANTA: Babu fargabar juyin mulki a ƙasar nan – Gwamnatin Najeriya

Congo Brazzaville ba ta cikin yankin Sahel, inda barazanar masu jihadi iƙirarin jihadi ta zama jiki, kuma wataƙila wannan raɗe-raɗin ya samo asali ne saboda daɗewar shugaban ƙasar na yanzu a kan mulki, ina ya jagoranci ƙasar a tsakanin shekarar 1979 zuwa 1992 sai kuma ya ci gaba daga 1997 har ya zuwa yanzu.

Ana sa ran Shugaba Denis Sassou-Nguesso zai halarci taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 78 wanda za a yi a Amurka daga ranar 18 zuwa 19 ga watan Satumba.

Leave a Reply