‘Yan sanda a Filato sun kama wata mata da ta saci jaririya

2
399

Rundanar ‘yan sandan jihar Filato ta gabatar da wata mata mai suna Patient Solomon da ake zargi da sace wata jaririya ‘yar wata 10.

An gabatar da matar ne a gaban jama’a tare da wasu ƙarin mutum 27 da ake zargi da aikata munanan laifuka a faɗin jihar.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Okoro Julius, wanda shi ne ya ajiye matar a hedikwatar ‘yan sanda da ke birnin Jos, ya bayyana cewa rundunar na ci gaba da himma domin tabbatar da an kawo ƙarshen ayyukan ɓata-gari a gari.

Kwamishinan ‘yan sandan ya bayyana cewa bayan gano jinjirar daga bisani an miƙa ta ga mahaifiyarta.

Mahaifiyar jaririyar mai suna Annabel Geoffrey ta shaida wa manema labarai yadda lamarin ya faru. Inda ta ce “ba ni da masaniyar ta tafi da ‘yata saboda a gida ɗaya muke zaune da ita”.

KU KUMA KARANTA: Mai rainon jariri ta saci jariri ɗan wata biyu lokacin yaye ɗalibai a makaranta a Kwara

“Bayan an ɗauki lokaci ban ga yarinyar ba, sai na ƙira lambar matar amma ƙiran ba ya shiga. Daga baya ta ƙira ni inda ta sanar da ni ta yi tafiya zuwa Legas tare da ‘yata.”

Ta ce bayan haka ne ta kai rahoton lamarin ga jami’an ‘yan sanda. Sai dai wadda ake zargin Patient Solomon ta musanta cewa satar jaririyar ta yi.

A cewarta, ta ɗauki yarinyar ne kawai saboda so da ƙauna ba wai da nufin cutar da ita ba.

2 COMMENTS

Leave a Reply