Daga Ibraheem El-Tafseer
An mayar da ‘yan Najeriya 298 da suka maƙale a Libya gida a cikin jiragen haya daban-daban a farkon makon nan.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA ta ce an mayar da su ne kai tsaye daga gidajen yarin Libya.
Galibin waɗanda aka mayar da su dai mata ne da suka shafe lokaci mai tsawo a sansanonin tsare mutane daban-daban a ƙasar da ke arewacin Afirka, wadda ke fama da rikici.
KU KUMA KARANTA: Libya ta kori baƙin haure 486 ba bisa ƙa’ida ba
A cikin waɗanda aka mayar gida akwai mata 119, waɗanda yawancinsu suna da ciki, tare da yara mata uku da jarirai biyu, sai kuma maza 170, yara maza uku, da jariri namiji ɗaya.
Hukumar Kula da Hijira ta Duniya (IOM) da Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) ne suka ɗauki nauyin mayar da su gida a ƙarƙashin shirin bayar da Kariya da Taimakon bakin haure.