Minista ta yi hasashen ambaliyar ruwa a wasu jihohi

1
242

Bayan buɗe madatsar ruwan Lagdo na ƙasar Kamaru, gwamnatin tarayya ta ce za a fuskanci ambaliyar ruwa mai tsanani a wasu jihohi nan da kwanaki bakwai masu zuwa.

Ministar harkokin jin ƙai da yaƙi da fatara, Betta Edu ce ta yi wannan hasashen a ranar Litinin ɗin da ta gabata a lokacin da ta karɓi baƙuncin ministar albarkatun ruwa, ministar muhalli, da sauran masu ruwa da tsaki kan hanyoyin da za a bi don daƙile illar ambaliyar ruwa a Najeriya.

Ministan ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za a samar da matsuguni ga mazauna jihohin da ke fama da ambaliyar ruwa.

KU KUMA KARANTA: Ambaliyar ruwa ya kashe mutane 32 a Nijar

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa an sanar da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) kan ambaliyar ruwa da ke tafe a gaɓar kogin Benuwe.

A cewar sanarwar, gwamnatin Kamaru na da shirin “buɗe ƙofofin ambaliya na Dam Lagdo a kan kogin Benuwe nan da kwanaki masu zuwa”.

1 COMMENT

Leave a Reply