Likitoci a Zamfara za su tsunduma yajin aiki kan rashin albashi

0
184

Daga Ibraheem El-Tafseer

Ƙungiyar likitocin Najeriya (NMA) reshen jihar Zamfara ta bai wa gwamnatin jihar wa’adin mako guda ta biya ma’aikatan lafiya 17 albashinsu na wata huɗu da sauran ma’aikatan lafiya a asibitin ƙwararru na Yarima Bakura ko kuma su shiga yajin aiki.

Shugaban NMA na jihar, Dakta Sanusi Bello, wanda ya yi wa manema labarai jawabi a ranar Litinin a Gusau, babban birnin jihar, ya kuma bayar da misali da albashin dukkan likitocin asibitin na watan Yuli 2023, da alawus na wata takwas ga ƙwararrun likitoci da ba a biya, wanda ya sa suka daina aiki.

Bello ya ce ƙungiyar ta yanke shawarar bayar da wa’adin mako guda ga gwamnatin jihar Zamfara domin ta magance wadannan bukatun.

Ya ƙara da cewa ƙungiyar a Zamfara za ta ci gaba da yajin aikin sai baba ta gani daga ranar Litinin 4 ga Satumba, 2023, idan har gwamnati ta ƙasa biya musu buƙatunsu.

Shugaban ya yi gargaɗin cewa matakin zai kai ga rufe dukkanin asibitocin da suka haɗa da asibitocin gwamnatin tarayya da asibitocin jiha da asibitoci masu zaman kansu da kuma janye duk wani aikin lafiya da na haƙori da duk likitocin jihar Zamfara ke yi.

Leave a Reply