Bankin Fidelity ta ba da gudummawar kayan agaji ga ‘yan gudun hijira a Filato

0
481

Bankin Fidelity Plc ta bayar da tallafin kayan agaji ga ‘yan gudun hijirar da ke ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Filato.

Da yake gabatar da kayayyakin a ranar Litinin a Jos, Mista Sadi Zawiya, shugaban bankin na Arewa ta tsakiya, ya ce sun ɗauki wannan mataki ne da nufin rage raɗaɗin da ‘yan gudun hijirar ke ciki a jihar.

Zawiya ya ƙara da cewa wannan karimcin wani ɓangare ne na ɗaukar nauyin da ya rataya a wuyan bankin.

“Wannan gudummawar ta kasance don sanin gaskiyar cewa nasarar da muka samu tana da alaƙa da jin daɗin al’ummomin da suka karɓi baƙuncinmu.

“Mun san waɗannan kayayyaki ba su kusa da abin da mutane suka yi asara ba, amma alama ce ta goyon bayan mu don rage wahalhalun da ‘yan gudun hijirar Mangu ke ciki.

KU KUMA KARANTA: NEMA ta ba da tallafin kayan agaji ga mutane dubu 23 a Nijar

“Muna addu’ar Allah ya dawo mana da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa kuma za mu ci gaba da tallafa wa al’ummar jihar da ke cikin mawuyacin hali,” inji shi.

Da yake karɓar kayayyakin a madadin waɗanda abin ya shafa, Gwamna Caleb Mutfwang, ya gode wa bankin da wannan karimcin.

Mista Mutfwang wanda mataimakinsa Josephine Piyo ya wakilta ya yi alƙawarin cewa kayayyakin za su kai ga duk waɗanda abin ya shafa.

Gwamnan wanda ya koka da yadda ake samun yawaitar kashe-kashe da ɓarnata gonaki da sauran kadarori a jihar, ya ce gwamnatinsa na ƙoƙarin ganin ta magance matsalolin tsaro.

Wasu daga cikin kayayyakin da aka bayar sun haɗa da; Katifu 100, barguna 100, tamanin roba 100, bokiti 120, kofuna 300, buhu 150 na shinkafa da buhunan garin masara 155.

Sauran sun haɗa da; Garri buhu 20, katon mai 50, garin madara 20 da silifas na banɗaki guda biyar.

Sauran kayayyakin sun haɗa da; Gishiri buhu 25, katan 20 na kayan yaji, buhu 20 na sukari, katon lipton guda biyar, katantan wanki 60 na sabulun wanki da kwali 40 na wanka da sauransu.

Leave a Reply