Connect with us

Labarai

NEMA ta ba da tallafin kayan agaji ga mutane dubu 23 a Nijar

Published

on

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA), ta bayar da tallafin kayayyakin agaji ga manoma da kuma marasa galihu 23,000 da ambaliyar ruwa na shekarar 2022 ta shafa a Nijar.

Babban daraktan hukumar Mustapha Ahmed ne ya bayyana haka a lokacin ƙaddamar da rabon kayayyakin tallafin a Minna ranar Asabar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ba da rahoton cewa an yi wa laƙabi da “Special National Economic and Livelihood Emergency Intervention (SNELEI)”.

Ahmed, wanda Abubakar Yusuf, mai kula da rabon kayayyaki ya wakilta, ya ce an ɗauki matakin ne don tallafa wa manoman da ambaliyar ruwa ta shafa a shekarar 2022 da kuma sauran waɗanda suka fi kowa rauni don daƙile illolin bala’in.

KU KUMA KARANTA: Hukumar NEMA ta ba da sanarwar ambaliyar ruwa ga al’ummomin Adamawa

“Ku tuna cewa abin baƙin ciki na bala’in ambaliyar ruwa na 2022 ya shafi al’ummomi da dama a faɗin ƙasar ciki har da Nijar,” in ji shi.

Malam Ahmed ya lissafa abubuwan da suka haɗa da; injin ɗinki da niƙa, buhunan shinkafa 25, buhunan wake da dawa 10, gishirin mai, buhunan tumatir da kayan yaji.

Sauran sun haɗa da gidajen sauro, tabarmar roba, barguna, bokitin robobi,  katifu, tukwane, sabulun wanka da na wanki da murhun dafa abinci.

Sauran sun haɗa da: masara da irin shinkafa, maganin kashe ƙwari, masu inganta girma, takin ruwa da fanfunan ruwa, da dai sauransu.

Mista Ahmed ya shawarci waɗanda suka amfana da su yi amfani da kayayyakin yadda ya kamata domin inganta zamantakewa da tattalin arziƙinsu.

A nasa jawabin, mataimakin gwamnan Neja, Garba Yakubu, ya yabawa hukumar (NEMA) kan yadda ta kasance a kodayaushe domin ceto waɗanda aka zalunta.

Mista Garba, wanda Bello Ibrahim ya wakilta, mataimakinsa, ya ce kayayyakin za su taimaka sosai wajen ƙara ƙaimi ga ƙoƙarin gwamnatin jihar na kawo agaji ga waɗanda abin ya shafa.

Tun da farko a jawabinsa na maraba, Garba Salihu, muƙaddashin darakta janar na hukumar bayar da agajin gaggawa ta Neja (NSEMA), ya yi alƙawarin cewa za a raba kayayyakin ga waɗanda abin ya shafa na gaske.

Ɗaya daga cikin waɗanda suka ci gajiyar tallafin, Suleiman Ibrahim, ya godewa gwamnatin tarayya bisa wannan karimcin, inda ya ƙara da cewa kayayyaki za su yi nisa wajen rage musu raɗaɗi.

Al'ajabi

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Published

on

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon bene mai hawa biyu a Jihar Legas, ya rushe yayin da ake tsaka da mamakon ruwan sama wanda ya haddasa ambaliya a wasu sassan jihar.

Ginin ya rushe ne a lamba 12 da ke yankin Cameroun kusa da Ewenla a Mushin.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (LASEMA), ta bayyana cewar bayan isar jami’anta wajen da lamarin ya faru, ta gano wani sabon gini mai hawa biyu ya rushe.

An ceto mutum bakwai; mata uku da maza huɗu, tuni aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.

KU KUMA KARANTA: Wani bene mai hawa 4 ya rufta da mutane a Abuja

Ya zuwa yanzu dai hukumar, ta ce babu wanda ya mutu a dalilin rushewar ginin.

Babban sakataren LASEMA, Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce ana ci gaba da gudanar aikin ceto don tabbatar da babu wanda ya maƙale a baraguzai.

Continue Reading

Labarai

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Published

on

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewar wani jami’in Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC), ya hallaka kansa har lahira a Abuja.

An tsinci gawar marigayin ne a gidansa da ke babban birnin tarayya.

Marigayin, wanda ba a bayyana sunansa ba, an ce ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka yi kwas na 5 a makarantar horas da masu yi wa ƙasa hidima ta hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa.

An ruwaito cewar yana da ƙwazo da himma a wajen gudanar da ayyukansa.

Wata majiya ta ce jami’in ya jima yana fama da baƙin ciki da matsalolin rayuwa kafin mutuwarsa.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya shaida wa manema labarai cewa hukumar za ta binciki musababbin da ya sanya ya kashe kansa, kuma hukumar za ta taimaka wa iyalansa.

Oyewale, ya ƙara da cewa hukumar za ta binciki wasu abubuwa da suka haɗa da matsalar taɓin hankali da kuma matsalolin iyali waɗanda ka iya sanya ma’aikacin kashe kansa.

KU KUMA KARANTA: Ana zargin wani jami’in kwastam ya kashe kansa a Abuja

Sai dai ya ce hukumar ba za ta fitar da wata sanarwa ko kuma bayyana sunan jami’in ba, har sai an kammala bincike.

Continue Reading

Labarai

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Published

on

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta rufe shaguna kusan 100 a babbar kasuwar Ogbete ta Jihar Enugu, bisa zargin sayar da wasu abubuwan sha na jabu.

Daraktan NAFDAC, Martins Iluyomade a yankin Kudu maso Gabas, ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne bayan wani samame da ta kai a ranar Litinin.

A yayin samamen jami’an hukumar NAFDAC, sun cafke wata babbar mota ɗauke da kayayyakin maye tare da cafke wasu ‘yan kasuwa huɗu da ake zargi da hannu wajen sayar da jabun abubuwan sha.

Iluyomade, wanda masanin haɗa magunguna ne, ya nanata cewa matakin ya zama dole domin kare masu amfani da ire-iren kayayyakin .

Ya ce waɗanda ake zargin a halin yanzu ana kan bincikensu kuma za su fuskanci tuhuma a gaban kotu bayan kammala binciken.

KU KUMA KARANTA: NAFDAC ta haramta amfani da maganin tari na yara na kamfanin J&J

Har wa yau, ya nanata ƙudurin NAFDAC na kawar da kayayyaki marasa inganci, da jabun abubuwan ci da sha, da gurɓatattun kayayyaki a kasuwa.

Ya ƙara da cewa, an gudanar da binciken ne tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro.

A gefe guda kuma, ya bayyana muhimmancin aikin hukumar na tabbatar da lafiyar al’umma.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like