Matashi ya rataye kansa a jihar Jigawa

0
265

Wani matashi, mai suna Samaila Ilu, ɗan asalin jihar Jigawa, mai shekaru 35, ya kashe kansa ta hanyar rataya.

Rahoton ya ce ya kashe kansa ne sakamakon mummunan halin da yake ciki na rayuwa, a jihar Jigawa.

DSP Lawan Shiisu Adam, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar DAILY POST.

A cewarsa, “A ranar 17/08/2023 da misalin ƙarfe 11:00 na safe ‘yan sanda sun samu rahoton cewa wani matashi mai suna Samaila Ilu mai shekaru 35 a ƙauyen Dungun Tantama a ƙaramar hukumar Kafin Hausa ya bar gidansa a ranar 16/08/2023 zuwa wani waje da ba a sani ba”

Daga baya ya bayyana cewa an gano gawarsa a rataye a jikin bishiya da igiya, wanda ke nuna cewa ya kashe kansa.

KU KUMA KARANTA: Yadda mahaifiyar ‘ya’ya 9 ta rataye kanta a Borno

Shiisu ya bayyana cewa, tawagar ‘yan sanda ta ɗauki gawar tare da kai ta asibiti domin a duba gawarwakin gawar.

Ya bayyana cewa yanzu an miƙa shi ga ‘yan uwansa domin yi masa jana’iza.

Leave a Reply