1- Ki nisanci duk wata ƙawa da za ta dinga bayyana miki tsaraicinta.
2- Ka da ki yarda ƙawarki ta yabaki ta fuskar sha’awa.
3- Ki guji ƙawar da za ta dinga rungume ki da nufin wasa.
4- Ki tsoraci ƙawar da za ta dinga kunna miki fina-finan ‘yan maɗigo (Lesbian).
5- Ka da ki yarda ƙawarki ta kama hannunki na tsawon lokaci don idan ta jima tana shafa miki hannu, da sannu za ta kai ga mabuɗin sha’awa, shi ne ta fara shafa miki ƙirjinki.
6- Ki nisanci ƙawar da za ta dinga yawan shafa gashin kanki.
.
7- Ki ƙauracewa ƙawar da za ta dinga yawan kwanciya ajikinki batare da wani dalili ba.
KU KUMA KARANTA: Kaciyar mata mugun abu ne – NGO
8- Ki ƙyamaci ƙawar da a ko da yaushe za ta dinga son ta dinga ganin jikin ki , kamar ƙirjin ki da bayan ki zuwa ƙasan marar ki.
9- Ki rabu da ƙawar da za ta dinga yawan yi mi ki kyaututtuka masu tsada ba bisa dalili ba.
10- Ki bar ƙawar da take yawan jan ki zuwa gidan ƙawayen ta waɗanda ba ki san su ba, kuma ba su da mazaje koma suna da mazajen, amma waɗanda kika ga suna yawan ƙulewa
cikin uwar ɗaka ko suke yawan tafawa suna rungumar juna, ko kwanciya akan cinyar juna ko suke yawan cire tufafinsu a gaban juna ko wanka tare.
11- Ki ƙyamaci ƙawar da ba ta da hira sai hirar mace ‘yar uwar ta.
12- Ki guji ƙawar da ba ta son yawan mu’amala da maza a matsayin samari ko masoyi, ta fi mu’amala da mace ‘yar uwarta.
13- Ki ƙauracewa ƙawar da take da sha’awar kallon fina-finan batsa musamman irin na mace da mace (Lesbian).
14- Ki fita sha’anin ƙawar da ake yaɗa jita-jitan tana maɗigo (Lesbian).
15- Ki rabu da ƙawar da take mu’amala da ƙawaye masu maɗigo (Lesbian) ko da ita ba ta yi, domin kallon mai yi ake yi nata kema haka za’a yi miki kallo.
16- Ki guji ƙawar da take zaman kanta agidan da ta kama take haya kuma mata ke taruwa a gidanta.
17- Ki fita sha’anin ƙawar da ba ta jin kunyar cewa aga-aga, na ƙirji ko baya ko ƙasan marar juna.
18- Ki haƙura da ƙawar da ‘yan madigo ke burgeta ko da ita ba ta yi.
19- Ki ƙyamaci ƙawar da take yawan yabon surorin jikinki irin ƙirjinki da mararki da bayanki.
20- Kiyi tir ki kuma guji tare da ƙyamatar ƙawar da kuna haɗuwa maimakon ta miƙo miki hannu kuyi musabiha sai dai takai hannu ta daki bayanki (Mazaunanki) ko ta ɗan shafa ƙirjinki.
Mata kuyi hattara don samun tsira daga wuta
Allah yasa mudace, ameen.