Nottingham Forest ta ɗauko Turner daga Arsenal

1
336

Daga Ibraheem El-Tafseer

Nottingham Forest ta amince da cinikin golan Arsenal Matt Turner.

Ɗan wasan na Amurka ya kasance mataiamakin Aaron Ramsdale amma yayin da Mikel Arteta ke ƙoƙarin sayen David Raya daga Brentford, Turner ya nemi damar ƙarawa gaba.

Ɗan wasan mai shekaru 29 ya kafa kansa a matsayin na ɗaya a tawagar Amurka kuma ya taka leda a gasar Gold Cup na baya-bayan nan inda suka kai matakin wasan kusa da na ƙarshe.

An fahimci cewa yunƙurin ɗauko Turner ba zai hana tataunawan da Forest ke yi kan sayen Dean Henderson na Manchester United ba, wanda koci Steve Cooper ke son dawo da shi filin City Ground.

Forest sun ɗauko aron Henderson da golan Paris St-Germain eylor Navas a kar wasan 2022-23, amma tuni suka koma ƙungiyoyinsu.

KU KUMA KARANTA: Mbappe ba zai yi atisaye da PSG ba

Cooper ya riga ya yi ƙarin wasa shida na dindindin a cikin tawagarsa a wannan bazarar, inda ya ɗauko Chris Wood da Will Brook da Harry Griffiths da Manni Norkett da Ola Aina da kuma Anthony Elanga.

1 COMMENT

Leave a Reply