Ƙwaro mafi kururuwa a duniya

1
219

Ƙwaron da ya fi kowane kururuwan ɗaga sauti a duniya shi ne “Cicada.” Bugu da ƙari, akwai wani irin kuwwa da suke yi don kusantar ahalinsu, ta yadda suke gane ‘yan uwansu ba tare da wani ya yi wa wani kutse ba.

Su na kuma rera waƙa a rukuni-rukuni don korar tsuntsaye ko wasu ƙwari da ke farautarsu da ƙarar sautinsu, su na kuma yin wani irin sauti da ake ƙira “Decibels” wadda ya yi kama da sautin fashewar gungumen dutse, ko injin jirgin sama mai sauƙar ungulu, ko kuma tsawa.

Akwai nau’in ƙwarin Cicada guda 1,300 a duniya, 150 daga cikinsu ana samun su a Afirka Ta Kudu (South Africa).

1 COMMENT

Leave a Reply