Na yi mamakin juyin mulki a jamhuriyar Nijar – Buhari

0
208

Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana kaɗuwarsa kan juyin mulkin da ya kifar da gwamnatin Mohammed Bazoum a jamhuriyar Nijar.

Tsohon shugaban ƙasar, ya ce ya yi farin ciki da cewa tuni shugaban ƙasa Bola Tinubu ya fara tuntuɓar ci gaban da aka samu domin kawo ƙarshen juyin mulkin.

Buhari ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ta shafinsa na Twitter ranar Juma’a.

Tsohon shugaban na Najeriya ya ce yana da ƙwarin gwiwa kan yadda Shugaba Tinubu zai iya magance rikicin.

KU KUMA KARANTA: An tabbatar da Sojoji sun yi juyin mulki a Nijar

Buhari ya tabbatar wa jama’a cewa Tinubu zai iya sauya lamarin tare da tabbatar da tsaron Bazoum da iyalansa.

Ya ce: “Kamar yadda ake tsammani, ni, kamar sauran miliyoyin ‘yan Nijeriya, na yi mamakin irin abubuwan da suka faru a Jamhuriyar Nijar.

“An nuna damuwa game da makomar dimokuraɗiyya a matsayin tsarin gwamnati a ƙasar nan da ma sauran yankuna, haka ma, game da lafiyar Shugaba Mohammed Bazoum da iyalansa.

“Ni da iyalina mun damu da waɗannan kamar kowa.

“Abin farin ciki ne ganin cewa ƙungiyar ECOWAS, ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ta rigaya ta shawo kan lamarin yadda ya kamata; “kuma fatanmu da addu’o’inmu shi ne cewa yanayin da ba a so ya koma gaba ɗaya, kuma an tabbatar da tsaro da jin daɗin Shugaba Bazoum da danginsa.”

Leave a Reply