Wani mutum ya sare kan ɗan shekara 84 a Ogun, shi ma ya mutu saboda ya ƙi yarda a kama shi

A ranar Juma’a ne wani mutum mai suna David Shodola mai shekaru 32 da ake zargin yana da taɓin hankali ya fille kan wani dattijo mai shekaru 84 mai suna Alfred Opadipe a unguwar Iperu da ke ƙaramar hukumar Remo ta Arewa a jihar Ogun.

Shi ma Mista Shodola ya mutu ne yayin da aka ce ya yi turjiya da kakkausar murya tare da kai wa jami’an ‘yan sanda hari da adduna.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Ogun, SP Omotola Odutola, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Abeokuta ranar Juma’a.

KU KUMA KARANTA: Ɗan fashin mota ya kashe jami’in kwastam a Kebbi

Odutola ya ce biyo bayan ƙiran da aka samu daga wani wanda bai so a bayyana sunansa ba, jami’an ‘yan sanda ƙarƙashin jagorancin jami’in ‘yan sanda na yankin Isara, DPO, Bankole Eluyeru, sun auka wa wurin.

PPRO ya ce an yi turjiya sosai a yunƙurin cafke wanda ake zargin yayin da ya yi amfani da “addar adduna ga jami’in ‘yan sanda na yankin da mutanensa.”

Kakakin ‘yan sandan ya ce rundunar ta yi nasarar kashe wanda ake zargin.

Odutola ya ce daga bayanan sirrin da ‘yan sanda suka tattara, babu wani rahoton cewa wanda ake zargin yana da taɓin hankali.


Comments

One response to “Wani mutum ya sare kan ɗan shekara 84 a Ogun, shi ma ya mutu saboda ya ƙi yarda a kama shi”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Wani mutum ya sare kan ɗan shekara 84 a Ogun, shi ma ya mutu saboda ya ƙi yarda a kama shi […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *