Kotu ta ba da umarnin a gaggauta sakin Emefiele

0
380

Daga Ibraheem El-Tafseer

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ce kamawa tare da tsare dakataccen gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele da DSS ke yi ya saɓa wa doka.

Yayin da yake yanke hukuncin, Mai shari’a Bello Kawu ya ce kamawa da kuma bincikar Emefiele, ya saɓa wa hukunci da kuma umarnin da wata kotun ta bayar na sakin sa.

KU KUMA KARANTA: Emefiele yanzu yana hannunmu – SSS

Lauyan Mista Emefiele, Peter Abang, ya nemi kotun da ta jingine sannan ta ayyana kamu tare da tsare shin da hukumar DSS ke yi a matsayin haramtacce.

Kasancewar a ranar 29 ga watan Disamban 2022 wata kotu ta dakatar da kama mista Emefiele.

Leave a Reply