An saka dokar taƙaita zirga-zirga na awa 24 a Mangun jihar Filato

0
357

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ya sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta sa’a 24 a ƙaramar hukumar Mangu na jihar sakamakon hare-hare da suka janyo asarar rayuka da ma dukiyoyi a yankin.

Rikicin tsakanin wasu ƙabilu a yankin ya kuma raba mutane da dama da muhallansu da kuma haifar da zaman ɗar-ɗar tskakanin ƙabilun fulani da kuma ta magafu.

Shugaban matasan Fulani ta Miyetti Allah a yankin na Mangu, Saidu Jauro ya faɗa wa BBC cewa al’ummar magafu sun kai hari a gidajen fulani tare da ƙona wasu, inda ya ce an kashe mutane 18 a garin Amsan.

Wani daga ɓangaren ƙabilar ta magafu da ake zargi da kai harin ya ce ‘a iya sanina ban san wani ɗan ƙabilar magafu da ya far wa fulani ba”.

Leave a Reply