Ƙungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya sauya dokar ba da bashin karatu ga ɗalibai da ya amince da ita, zuwa tallafin karatu domin bai wa ɗalibai masu ƙaramin ƙarfi damar samun ilimi mai zurfi.
A wata hira da gidan Talbijin na Channels ranar Lahadi, shugaban ASUU ya ce bashin karatun ba abu ne mai yiwu ba. A cewarsa, bayar da bashi don yin karatu “ba zai ɗore ba”.
Farfesa Emmanuel Osodeke ya ce, “tunanin bayar da bashin karatu ga ɗalibai ya zo ne a 1972 kuma yana cikin harkokin bankuna da aka kafa”.
KU KUMA KARANTA: NURTW ta goyi bayan shugaba Tinubu kan cire tallafin man fetur
Ya yi iƙirarin cewa mutanen da suka karɓi bashin, ba su taɓa biya ba, kuna iya zuwa ku bincika. A shekarar 1994 ko 1993, sojoji sun kafa dokar soja mai lamba inda suka kafa hukumar bayar da bashi ga ɗalibai. Sai Majalisar dokoki ta daidaita ta a shekara ta 2004 kuma a cikin shekara ɗaya, ta wargaje. Kuɗaɗen suka ɓace. Muna so mu ga yadda wannan zai bambanta”.
A cewarsa, akwai ɗalibai sama da miliyan ɗaya a jami’o’in gwamnatin Najeriya kuma rancen ba zai iya biyan kuɗin karatun ɗalibai ba.
A ranar Litinin ne Shugaba Tinubu ya sa hannu a kan dokar ba da bashi ga ɗalibai domin cika alƙawarin da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓensa.
Shugaban majalisar wakilai ta 9, Femi Gbajabiamila, wanda yanzu shi ne shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa ne ya ɗauki nauyin gabatar da ƙudurin dokar a majalisa.
Dokar ta tanadi ba da bashi maras ruwa ga ɗalibai masu ƙaramin ƙarfi a Najeriya.
[…] KU KUMA KARANTA: A bawa ɗalibai tallafin karatu, ba bashin kuɗin karatu ba – ƙiran ASUU ga gwamnatin tarayya […]
[…] KUMA KARANTA: A bawa ɗalibai tallafin karatu, ba bashin kuɗin karatu ba – ƙiran ASUU ga gwamnatin […]
[…] KUMA KARANTA: A bawa ɗalibai tallafin karatu, ba bashin kuɗin karatu ba – ƙiran ASUU ga gwamnatin […]
[…] KU KUMA KARANTA: A bawa ɗalibai tallafin karatu, ba bashin kuɗin karatu ba – ƙiran ASUU ga gwamnatin tarayya […]