Ana ta ce-ce ku-ce a ƙasar Tanzaniya bayan da aka gano wata mata mai matsakaicin shekaru ta yi wa wani yaro ɗan shekara takwas fyaɗe tare da shafa masa cututtukan da ake yaɗawa ta hanyar jima’i.
A ranar Juma’a ne aka yanke wa Desderia Mbwelwa, mai shekaru 57 hukuncin ɗaurin shekaru 29 a gidan yari, sai dai kawo yanzu ba a bayar da cikakken bayani kan hukuncin ba.
A ranar da lamarin ya auku, matar ta tarar da yaron a lokacin da yake kiwon shanu a wani ƙauye da ke kudancin yankin Iringa, sai ta tambaye shi inda abokansa suke.
KU KUMA KARANTA: Yadda mutum huɗu suka yi wa Yarinya fyade saboda laifin babanta
Sannan an ce ta yi lalata da shi a ƙarƙashin wata bishiya bayan ya ce abokansa ba su kusa.
Shari’ar dai ta samu shaidu biyar ciki har da wani likita da ya duba yaron ya kuma tabbatar da cewa ya samu raunuka kuma ya kamu da cutukan da ake samu ta hanyar jima’i sakamakon gurɓacewar da aka samu a al’aurarsa.
An ce Mbwelwa ta kare kanta da cewa ita babba ce mai ‘ya’ya da jikoki waɗanda suka dogara da ita.
Lauyanta, Frank Mwela, ya ce yana shirin ɗaukaka ƙara a kan hukuncin saboda ba a gwada wanda yake karewa ba don tabbatar da ko da gaske tana da cututtukan da ake ɗauka ta jima’i.
“Ba a gwada wadda nake karewa ba ko tana ɗauke da waɗannan cututtuka, inda da wanda nake karewa da mai shaidarta sun tabbatar da cewa ba su ɗauke da wata cuta saboda ɗaya daga cikin waɗanda suka yi shaida mijinta ne,” inji shi.
[…] KU KUMA KARANTA: Kotu ta ɗaure wata mata mai shekaru 57, kan laifin yi wa yaro ɗan shekara 8 fyaɗe […]
[…] KU KUMA KARANTA: Kotu ta ɗaure wata mata mai shekaru 57, kan laifin yi wa yaro ɗan shekara 8 fyaɗe […]