‘Yan bindiga sun kai hari kan tawagar motocin gwamnan Kogi Yahaya Bello, da yawa sun jikkata

2
288

Gwamnatin Kogi a ranar Asabar ce wasu ‘yan bindiga sun kai wa ayarin motocin Gwamna Yahaya Bello hari a kan babbar hanyar Abuja zuwa Lokoja.

Ta ce an kai harin ne a kusa da wani sansanin sojin ruwa mai nisan kilomita kaɗan daga Lokoja, babban birnin jihar.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kogi Kingsley Fanwo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Lokoja.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mata biyu, shugabannin jam’iyyar APC a Kaduna

Mista Fanwo ya yi zargin cewa ‘yan bindigar ‘yan barandan siyasa ne na wata jam’iyyar adawa a jihar, wato Social Democratic Party, (SDP).

Kwamishinan ya ce lamarin da ya faru da misalin ƙarfe 12:30 na rana, ya yi sanadin jikkatar mutane da dama da suka haɗa da jami’an tsaro tare da kai su asibiti domin kula da lafiyarsu.

“’Yan bindigar da ake zargin ‘yan bangan siyasa ne na jam’iyyar SDP, da suka hango ayarin Bello suna nufowa, sai suka tare hanya suka fara harbin ayarin.

“Wani Tundra mai ɗauke da tambari da tutocin jam’iyyar shi ma ya tare motar gwamnan kuma waɗanda ke cikin motar na ɗauke da bindigogi.

“Amma alhamdulillahi gwamnanmu ya bar wurin ba tare da wata matsala ba, kuma babu wani abin da zai tayar da hankali.

“Wasu mataimakan tsaro da sauran masu taimaka wa gwamnan sun samu raunuka, kuma an garzaya da su asibitocin neman kulawa na gaggawa.

“Muna ƙira ga jama’ar Kogi da su kwantar da hankalinsu domin jami’an tsaro suna da cikakken iko don tabbatar da kama ‘yan bindigar da suka kai harin,” in ji shi.

Mista Fanwo ya ce gwamnatin jihar ba za ta amince da taɓarɓarewar doka da oda ba, amma za ta yi duk mai yiwuwa don gurfanar da maharan a gaban ƙuliya manta sabo.

A cewarsa, gwamnan ya yi gargaɗin cewa kada wani ɗan jam’iyyar APC ya shiga cikin duk wani harin ramuwar gayya saboda rashin tsaro daga kowane ɓangare zai fuskanci hukunci mai tsanani.

Da yake mayar da martani, Kunle Afolayo, mai taimaka wa ɗan takarar gwamna na SDP na jam’iyyar SDP, Yakubu Ajaka, ya musanta zargin yana mai cewa: “Akwai kuma saboda ‘yan barandan siyasarsa ne suka kawo mana hari.”

“Shin zai yiwu jam’iyyar siyasa ta adawa ta kai wa gwamna hari haka? “Muna kan hanyarmu ta fadar Maigari da ke Lokoja daga Koton Ƙarfe da yammacin yau, sai ayarin motocin gwamnan da suka nufi Lokoja daga Abuja suka same mu a hanya, suka kai mana hari kamar haka.

“Allah ya san gaskiya. Abin takaici ne yadda gwamnatin APC a Kogi ke amfani da ƙarfin gwamnati a kanmu da kuma yi mana ƙarya kan laifin da suka yi mana,” in ji mai taimaka wa kafafen yaɗa labarai.

2 COMMENTS

Leave a Reply