Matawalle ya wawure motoci 17, injinan gas, da na’urorin talabijin na jami’an gwamnati – Gwamna Dauda

1
511

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya zargi tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle, da yin awon gaba da motocin gwamnati guda 17, tare da wawure dukiyoyi da suka haɗa da na’urorin talabijin da injinan gas na masu dafa abinci a gidan gwamnatin jihar.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa gwamna Lawal bayan rantsar da shi, ya bayyana cewa magabacinsa ya bar asusun jihar da bashi mai ɗimbin yawa.

Da yake magana a wani shirin wayar da kan jama’a a gidan rediyon Vision FM a Gusau, babban birnin jihar, gwamnan ya ce magabacinsa ya yi iƙirarin cewa motocin da aka sace kayansa ne.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Zamfara Dauda Lawal, ya sanar da kadarorinsa naira tiriliyan tara

Sai dai ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta yi iya ƙoƙarinta wajen ganin an gyara matsalar.

Ya ce, “Tsohon gwamna Bello Matawalle ya tafi da motoci 17 daga ofishinsa. Mataimakin gwamnan ya kuma yi iƙirarin cewa motocin jami’an da aka maƙala a ofishinsa kayan sa ne.

Hasali ma kayan ofis ma ba a tsira ba. “Ta’addancin ya wuce fahimta, ban taɓa ganin rashin alhaki irin wannan ba.

Amma, tare da kyakkyawan shiri, ina tabbatar wa ‘yan jihar cewa za mu yi iya ƙoƙarinmu don gyara abubuwan da ba su dace ba,” in ji gwamna Lawal.

1 COMMENT

Leave a Reply