‘Yan bindiga sun kashe mutane 18 a Benuwe

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari ƙauyen Iye da ke ƙaramar hukumar Guma a jihar Binuwai inda suka kashe mutane 18.

An ce ƙauyen yana bayan Jami’ar Joseph Sarwuaan Tarka, Makurdi, JOSTUM.

Mazauna ƙauyen sun shaida wa manema labarai cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 7 na dare.

Da yake tabbatar da harin, mashawarcin jami’an tsaro na ƙaramar hukumar Guma, Christopher Waku, ya ce mutane 18 ne suka mutu yayin da wasu da dama kuma suka jikkata a yayin harin.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe manoma tara a Kaduna

Mista Waku ya ce: “An kashe mutane 18 a ƙauyen Iye da ke ƙaramar hukumar Guma a jiya (Lahadi) tsakanin ƙarfe 6 zuwa 7 na yamma.

Ƙauyen yana bayan UniAgric, JOSTUM.” Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, PPRO, Catherine Anene, ita ma ta tabbatar da harin.

Misis Anene, ta ce an gano gawarwaki bakwai a safiyar ranar Litinin, yayin da ɗaya daga cikin maharan kuma ya mutu.


Comments

One response to “‘Yan bindiga sun kashe mutane 18 a Benuwe”

  1. […] KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe mutane 18 a Benuwe […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *