Dalilin da ya sa na amince da Tajudeen Abbas akan Betara – Zulum

2
248

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana dalilin da ya sa ya amince da Tajudeen Abbas a matsayin kakakin majalisar wakilai a kan wani ɗan takarar jihar Borno, Mukthar Betara.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa jam’iyyar APC mai mulki ta naɗa Abbas wanda ya fito daga jihar Kaduna da Benjamin Kalu daga Abia a matsayin kakakin majalisa da mataimakinsa.

Amma Betara, wanda ke wakiltar mazaɓar tarayya ta Biu/Bayo/Shani ta jihar Borno, tare da wasu ‘yan takara, sun yi fatali da tsarin shiyya-shiyya na jam’iyyar.

Da yake jawabi yayin ziyarar ban girma da Abbas da Kalu suka kai a Abuja, gwamnan Borno ya ce da ya so ace mataimakin shugaban ƙasa da kakakin majalisar sun fito daga jiharsa amma ba zai saɓawa shawarar da jam’iyyar ta yanke ba.

KU KUMA KARANTA: Kasancewar Shettima a matsayin mataimakin shugaban ƙasa, nauyin Borno da yawa zai ragu a kaina – Zulum

“A matsayinmu na mutanen Borno, da mun yi matuƙar farin ciki da alfahari da samun mataimakin shugaban ƙasa da kakakin majalisa. Amma tunda jam’iyya da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa sun amince da ku, in sha Allahu, za ku zama kakakin majalisa da mataimakinsa,” in ji gwamna Zulum.

Gwamnan ya buƙaci ’yan takarar jam’iyyar da su miƙa hannun zumunci ga sauran masu neman muƙami ɗaya. Tawagar ta kuma ziyarci gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, da takwaransa na jihar Filato, Simon Lalong.

Gwamnonin sun shawarce su da su samar da shugabanci mai dunƙulewa idan har suka zama shugabannin majalisar wakilai.

“Ina da biyu daga cikin nawa (‘yan majalisa daga Filato) waɗanda su ma suka nuna sha’awarsu. Amma na ba ku masu sauraro damar ganin ku. Kuma na gan ku.

“Lokacin da na ce na gan ku, kun san abin da nake nufi. Amma idan ka zama kakakin majalisa kuma mataimaki, dubi wasu abubuwan da muke buƙata a shiyyar Arewa ta tsakiya,” in ji Mista Lalong.

2 COMMENTS

Leave a Reply