Na nemi kotu ta raba auren mu, saboda mijina manemin mata ne – mata

0
274

Wata mata ‘yar shekara 44 mai suna Oluwatoyin Falade, a ranar Larabar da ta gabata ta kawo ƙara a wata kotun gargajiya ta Orile Agege akan ta raba aurenta da ta shafe shekara 11 bisa laifin rashin aminci da mijinta, Segun ya yi.

Mai shigar da ƙarar, wacce ke da shekaru 23, Tunde Davids Close, Agege, Legas  tana da ‘ya’ya biyu na Segun, masu shekaru takwas da 11.

“Mijina manemin mata ne, yana bin duk macen da ya gani.

“Ina da ‘yan mata biyu kafin na aure shi, kuma ‘yan matan sun kasance 15 da 18. Suna zama tare da ni kuma ban amince da mijina ba saboda yana bin duk macen da ya gani.

“Mijina yana canza mata ko ta yaya kuma baya girmama ni. Idan kotu ba ta raba auran ba, zan gudu da ’ya’yana,” ta fashe da kuka.

KU KUMA KARANTA: Ban amince kotu ta raba aurenmu ba, ina son matata – miji

Misis Oluwatoyin ta ce mutane suna yi mata ba’a a unguwar saboda rashin ɗa’an mijinta.

“Na ƙosa, Segun ba zai iya canzawa ba, bin mata ya zama mishi jiki” in ji ta. Ta yi zargin cewa ba ya kula da ita da yaran.

A martanin da ya mayar, Segun, mai shekaru 46, ma’aikacin shari’a a jihar Legas, ya amince da aikata laifin da yayi. “Ba zan yi ƙarya ba, ina kawo mata daban-daban a gidan amma a shirye nake in canza.

Na daɗe ina roƙon ta da ta yi min gafara,” inji shi. Yace yana kula da yaran da matarsa. “Ubangijina, kana iya ganin matata tana da ƙarfi da sabo.

A bayyane yake cewa ba ta wahala. “Na saya mata waya kwanan nan kuma na biya kuɗin makarantar yara,” in ji shi. Segun ya ce bai shirya rabuwa da ita ba, ya kuma yi alƙawarin gyara al’amura idan aka sake ba shi dama.

Shugaban Kotun, Adewale Adegoke, ya shaida wa ɓangarorin biyu da su zauna lafiya da juna. Mista Adegoke ya ɗage ci gaba da sauraron ƙarar har zuwa ranar 30 ga watan Mayu don wata hanyar warware taƙaddamar.

Leave a Reply