Bana za a samu ambaliyar ruwa a jihar Ekiti – NEMA

0
221

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa, (NEMA), ta shawarci mazauna jihar Ekiti da su ɗauki matakan kariya domin kaucewa ambaliyar ruwa da aka yi hasashen zai auku a jihar nan gaba a wannan shekara.

Shugaban ayyuka na NEMA a jihohin Ekiti da Ondo, Ƙadiri Olanrewaju ne ya yi wannan gargaɗin yayin wani taron wayar da kan jama’a da aka gudanar a kasuwannin Oja-Bisi, Oja-Oba da Fayose ranar Laraba a Ado-Ekiti.

Mista Olanrewaju ya ce hasashen da hukumomin da abin ya shafa ya sanya jihar Ekiti cikin jihohin da ake sa ran za su fuskanci ambaliyar ruwa sakamakon ƙaruwar ruwan sama.

KU KUMA KARANTA: Za a samu ambaliyar ruwa a jihar Kwara – NEMA

Ya ce galibin ƙananan hukumomin jihar na fama da ambaliyar ruwa tare da yin kasada sosai sakamakon ruwan sama da aka yi a lokaci guda.

Shugaban hukumar ta NEMA ya ƙara da cewa wayar da kan ‘yan kasuwar kan haɗarin ambaliya da yaruka daban-daban kamar Ingilishi da Pidgin da Igbo da Hausa da kuma yaren Ekiti shi ne maƙasudin gudanar da taron.

Ya ce, “Kowannenmu ya shaida yadda ambaliyar ruwa ta auku a Najeriya a baya-bayan nan, wadda ta yi sanadin salwantar rayuka, da raba dubban mutane, tare da lalata dukiyoyi na miliyoyin naira.

“Ambaliya tana haifar da ɓarkewar muhalli. “Saboda haka, ya zama dole ga al’umma, ɗaiɗaikun mutane da hukumomi su ɗauki matakan da suka dace.

“Muna buƙatar mu yi imani cewa rigakafin ya fi kyau kuma mai rahusa fiye da magani, tare da la’akari da batutuwan sauyin yanayi da mahimmanci.”

Mista Olanrewaju ya buƙaci ‘yan Najeriya da su yi biyayya ga gargaɗin da ma’aikatar yanayi ta yi kan ambaliyar da ke tafe, yana mai cewa hakan zai taimaka matuƙa wajen rage illar ambaliyar.

Hakazalika, Babban Manaja na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Ekiti, Jide Borode, ya shawarci ‘yan kasuwa da su guji ɗabi’ar zubar da shara a magudanun ruwa.

Har ila yau, Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Ekiti, Andrew Famosaya, ya buƙaci mazauna Ekiti da su daina sare bishiyoyi ba bisa ka’ida ba.

Ya ce a maimakon haka ya kamata mazauna yankin su riƙi noma da dashen itatuwa don hana sare dazuzzuka, wanda zai iya haifar da ambaliya.

Leave a Reply