Jami’ar ATBU ta hana shigar nuna tsaraici ga ɗalibai

3
584

Jami’ar Abubakar Tafawa Ɓalewa dake Bauchi, (ATBU), ta ce daga yanzu za ta ɗauki mataki a kan duk ɗaliban da suka saɓa wa ƙa’idojinta na shigar rashin ɗa’a da tufafi a jami’ar kamar yadda yake ƙunshe a kundin dokokin ɗaliban da aka yi wa kwaskwarima.

Dokokin da aka yi wa kwaskwarima na ƙunshe ne a cikin wata takarda ta cikin gida mai ɗauke da sa hannun shugaban kula da harkokin ɗalibai na jami’ar, Farfesa U.S. Abdullahi, mai kwanan wata 27 ga watan Afrilu kuma aka miƙa wa shugaban ƙungiyar ɗaliban jami’ar da dukkan ɗaliban jami’ar.

Shugaban jami’ar ya gargaɗi ɗaliban da al’ummar jami’ar kan karya ƙa’idojin da aka amince da su a yayin taron majalisar dattawa karo na 161 na cibiyar da aka gudanar a ranar 13 ga Afrilu, 2023.

KU KUMA KARANTA: Jami’ar Najeriya ta yi tayin karɓar dalibai daga Sudan da yaƙi ya hana ci gaba da karatu

Takardar ta ci gaba da cewa: “Na rubuto ne domin sanar da ku cewa Majalisar Dattawa ta Jami’ar ta amince da sabunta littafin Jagoran ɗalibai a taronta na yau da kullum na Majalisar Dattawa karo na 161 da aka gudanar a ranar Alhamis, 13 ga Afrilu, 2023.

Kamar yadda bayanin da REF:ATBU/SAD/SUG/VOL 11/0113 ya wallafa a shafin Facebook na jami’ar, ya nuna cewa duk ɗalibin da aka samu da laifi zai iya fuskantar horon tsawon zango ɗaya ko biyu, gwargwadon laifin da ya aikata.

Takardar ta kuma ce taɓawa, sumbata, runguma, yin tausa, ko zama a kan cinyoyin juna suna jawo rugujewar zangonnin karatu biyu.

Bayanin ya ci gaba da cewa gashin mata masu launuka iri-iri, ƙulle-ƙulle, yin tuƙi na ganganci, zane-zane a jiki, da huda hanci, ido da baki suna jawo dakatarwar zangon karatu ɗaya.

Sauran laifuffukan sun haɗa da sanya wando ɗamamme, tufafi shara-shara ga mata, kitson gashi ga ɗalibai maza, da gajeren wando, da sauran laifuka kuma suna jawo dakatarwar zangon karatu ɗaya.

A lokacin da aka tuntuɓi babban sakataren ƙungiyar ɗaliban, SUG, reshen ATBU, AbdulRauf Al-Amin, ya tabbatar da sahihancin bayanin. Ya ce, duk da haka, sabbin dokokin ba baƙo ba ne ga ɗaliban.

“Mun samu wannan bayanin daga jami’ar a makon da ya gabata, wanda ni da kaina na raba wa ɗaliban a ɓangarori daban-daban; yawancin abubuwan da ke ƙunshe ba sababbi ba ne, an yi nazari ne kawai,” inji shi.

3 COMMENTS

Leave a Reply