Kotun ɗaukaka ƙara za ta yi hukunci a kan sake zaɓen Ado Doguwa

2
360

Kotun ɗaukaka ƙara ta ajiye hukunci a ƙarar da jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) da ɗan takararta Salisu Yushau suka shigar na neman Alhassan Doguwa na jam’iyyar All Progressives Congress, (APC).

Wani kwamitin mutane uku na kotun ɗaukaka ƙara ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Ita George-Mbaba, ya keɓe hukuncin zuwa ranar da za a sanar da ɓangarorin jim kaɗan bayan da dukkan lauyoyin suka amince da muhawarar tasu a cikin ƙarar.

A ranar 7 ga watan Afrilu ne kotun sauraren ƙararrakin zaɓe ta Majalisar Dokoki ta ƙasa da ta Jiha ta yi fatali da ƙarar da NNPP ta shigar na neman hana INEC gudanar da ƙarin zaɓe a mazaɓar Tudun Wada/ Doguwa ta tarayya a jihar.

KU KUMA KARANTA: Za a sake zaɓe a mazaɓar Ado Doguwa

Yushau da NNPP na neman kotun ta yi watsi da hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaɓe na Majalisar Dokoki ta ƙasa da ta Jiha wadda ta ce ba ta da hurumin dakatar da INEC daga gudanar da zaɓen na karawa.

Masu shigar da ƙara a cikin buƙatar nasu sun kuma buƙaci kotun da ta yi watsi da zaɓen da aka yi ranar 15 ga watan Afrilu wanda ya ayyana Ado Doguwa a matsayin wanda ya lashe zaɓen mazaɓar tarayya ta Tudun Wada/ Doguwa.

Waɗanda ake ƙarar su ne: Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, (INEC), Alhassan Doguwa, memba mai wakiltar Tudun Wada/ Doguwa a Kano da APC a birnin tarayya.

Lauyan wanda ya shigar da ƙara, Adegboyega Awomolo SAN, ya ce sun shigar da ƙarar nasu na farko ne a ranar 25 ga watan Afrilu, tare da rubuta wasiƙar da suka buƙaci kotun ta ba da damar ɗaukaka ƙarar sannan ta yi fatali da waɗanda ake ƙaran na farko.

“Idan aka yi sanarwar ƙarshe da dawowar ɗan takara a matsayin wanda ya yi nasara kuma babu wata adawa ga hukuncin da INEC ta yanke to za a iya shigar da ƙarar zaɓe kamar yadda sashe na 24 (4) na dokar zaɓe ta 2022 ya tanada.

“Idan aka gudanar da zaɓen da ba a gama ba, ba za a yi zaɓe ingantacce ba har sai an kammala.” Lauyan wanda ake ƙara na farko, Idris Yakubu, ya shigar da ‘yar gajeriyar hujja mai ɗauke da kwanan wata 25 ga Afrilu, sannan ya buƙaci kotun da ta yi watsi da ƙarar.

Lauyan wanda ake ƙara na biyu da na uku, Nureini Jimoh, SAN, da kuma Abdul Adamu-Fagge, sun ce sake zaɓen ya sha bamban da na ƙarin zaɓen, don haka sun buƙaci kotun da ta yi watsi da babbar ƙarar a kotun, sannan ta yi watsi da ƙarar da kuɗin.

“INEC ta ce da zarar an kammala zaɓe bai kamata a ajiye shi a gefe ba kamar yadda sashe na 84 da 24(6) na dokar zabe ya tanada.

2 COMMENTS

Leave a Reply