‘Yan sanda sun kama ‘yan fashi 44 a Kano

1
244

Daga Haruna Yusuf

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wasu mutane 44 da ake zargin ‘yan fashi da makami ne da dillacin ƙwayoyi da ’yan daba a cikin kwanaki 10 na ƙarshen watan Ramadan a wani rangadi da suke yi a babban birnin jihar.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar wa manema labarai kamen a ranar Alhamis.

Ya ce, tawagar ‘Operation Restore Peace’ da ƙoƙarin rundunar ‘yan sandan jihar Kano ne suka kama su daga duk wani nau’i na laifuka, musamman matsalar ‘yan daba, shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da sauran munanan ɗabi’u.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun daƙile fashi a Abuja, sun kama wanda ake zargi

“Ayyukan share fage da rundunar ‘Operation Restore Peace’ ƙarƙashin jagorancin CSP Bashir Musa Gwadabe, jami’in rundunar ‘yan sanda ta Anti-Daba ta gudanar a cikin wannan kwanaki goma na ƙarshen watan Ramadan, ya kai ga kama mutum Arba’in da huɗu (44), ‘yan daba da dillalan ƙwayoyi.

“Dukkan waɗanda ake zargin daga adireshi daban-daban a cikin birnin Kano, an kama su da muggan makamai, miyagun ƙwayoyi, fashi da kuma sace dukiyoyi.

Za a gurfanar da waɗanda ake zargin zuwa kotu bayan an kammala bincike,” in ji Kiyawa. Ya ƙara da cewa, gabanin shirye-shiryen bukukuwan Sallah na shekarar 2023 mai zuwa, kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Mamman Dauda, ​​ya yi gargaɗin cewa duk wanda aka samu da wani makami a lokutan bukukuwa za a kama shi.

“Ya kuma yi ƙira ga duk masu aikata laifuka da su tuba ko su bar Jihar gaba ɗaya. Idan ba haka ba, za a kama su kuma su fuskanci fushin doka. Ya godewa al’ummar jihar Kano nagari bisa goyon baya, fahimta, ƙarfafa gwiwa, da haɗin kai.

“Ya buƙaci mazauna yankin da su yi wa Jiha da ƙasa addu’a kuma su kai rahoto ofishin ‘yan sanda mafi kusa, kuma ka da su ɗauki doka a hannunsu.

Za a ci gaba da sintiri da kai hare-hare a maɓoyar ’yan ta’adda a duk faɗin Jihar, saboda rundunar za ta ci gaba da ɗaukar lokaci wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.

1 COMMENT

Leave a Reply