Ta sayar da jaririnta ɗan wata 18 a kan kuɗi Naira 600,000 a Ogun – ‘Yan sanda

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta tabbatar da cafke wata mata ‘yar shekara 33, bisa zarginta da sayar da jaririnta mai watanni 18 a kan kuɗi Naira dubu 600,000 a yankin Sango-Ota da ke jihar.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa a Sango-Ota a ranar Litinin, ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abimbola Oyeyemi. “Har yanzu ‘yan sanda ba su gano wanda ake zargin ya sayi jaririn ba.

An kama wanda ake zargin ne biyo bayan ƙorafin da mijin matar, Nureni Rasaq ya shigar a Hedikwatar ‘yan sanda shiyya ta Sango.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da jami’in kula da zirga-zirgar ababen hawa a Ogun

“Rasaq, ya ruwaito cewa matarsa ​​ta bar gida zuwa Legas a ranar 15 ga Maris, tare da jaririyarsu amma ta dawo gida ba tare da jaririn ba.

“Ya ce duk kokarin da aka yi na sanin abin da ya faru da jaririn ya ci tura saboda matar ta ka sa bayar da cikakken bayani game da inda jaririn yake,” in ji kakakin ‘yan sandan.

Oyeyemi ya ce bisa wannan ƙorafin, jami’in ‘yan sanda na shiyya ta Sango, CSP Ɗahiru Saleh, ya yi ƙarin bayani ga jami’an da suka gudanar da bincikensa domin bin sawun matar kuma ba tare da ɓata lokaci ba aka kama ta.

Ya ƙara da cewa da ake yi masa tambayoyi, wadda ake zargin ta amsa cewa ta sayar da jaririn ga wani a Legas a kan kuɗi Naira 600,000.

Oyeyemi ta ce da aka tambaye ta dalilin da ya sa ta sayar da jaririnta, wanda ake zargin ya ce ta ci bashin kuɗi ne a wani banki mai ƙaramin ƙarfi, kuma da ta ka sa biyan kuɗin, sai jami’an bankin suka fara yi mata barazana.

“Ta gudu zuwa Legas ta fara sharar ruwan buhu. A cikin aikin ne ta haɗu da wani mutum, wanda ya gabatar da ita ga matar da a ƙarshe ta sayi yaron,” in ji shi.

Muƙaddashin kwamishinan ‘yan sandan jihar, DCP Babakura Muhammed, ya bayar da umarnin a miƙa wanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar domin ci gaba da bincike da kuma yiwuwar dawo da jaririn.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *