INEC ku sanar da Fintiri a matsayin wanda lashe zaɓen gwamnan Adamawa – PDP

Jam’iyyar PDP ta yi ƙira ga hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC da ta dawo da tattara sakamakon zaɓen gwamnan Adamawa tare da bayyana ɗan takarar jam’iyyar Ahmadu Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Jam’iyyar ta yi wannan ƙiran ne a wani taron manema labarai da sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Debo Ologunagba ya yi a Abuja ranar Lahadi. Mista Ologunagba ya ce sakamakon da aka ɗora a tashar INEC, IREv, tuni ya nuna cewa Fintiri ne ya lashe zaɓen.

“Saboda haka PDP ta buƙaci hedikwatar INEC da ta gaggauta umurci jami’in zaɓe da ya kammala tattara sakamakon zaɓe, ya bayyana sakamakon zaɓe a rumfunan zaɓe tare da bayyana ɗan takararmu, Mista Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaɓen, bayan da ya samu rinjayen ƙuri’un da aka kaɗa.

KU KUMA KARANTA: Ramadan: Gwamnatin Kano ta amince da hutun mako 3 ga makarantu

“Daga sakamakon da aka tattara a rumfunan zabe 69 da aka gudanar da zaɓukan ƙarara waɗanda ke kan tashar sakamakon zaɓen INEC (IReV), Fintiri ya lashe zaɓen.

“Don haka jam’iyyarmu ta buƙaci INEC ba tare da ɓata lokaci ba, ta bayyana sakamakon zaɓe kamar yadda aka riga aka tattara daga rumfunan zaɓe sannan ta bayyana Fintiri a matsayin wanda ya yi nasara.

“Duk abin da ya rage daga wannan ba zai samu karɓuwa daga jam’iyyarmu da al’ummar jihar Adamawa ba,” inji shi.

Mista Ologunagba ya yi Allah-wadai da matakin da hukumar zaɓe ta INEC reshen jihar Adamawa, REC, ta ɗauka, a matsayin haramtacce wanda ya tabbatar da zargin da jam’iyyar ta yi a baya na haɗa baki da kuma buƙatar a tsige shi cikin gaggawa.

Ya kuma yi ƙira ga Sufeto Janar na ‘yan sandan da ya gaggauta kamo Yunusa Ari tare da hukunta shi kan yadda doka ta tanada.

“PDP ta lura da shelar da hedikwatar INEC ta yi cewa matakin da Mallam Yunusa Ari ya yi ba shi da wani tasiri.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *