An yi garkuwa da wani jami’in hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Ogun (TRACE), Popoola Olasupo a ranar Lahadin da ta gabata a hanyar Fidiwo da ke kan hanyar Legas zuwa Ibadan.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya kawo an yi garkuwa da Olasupo ne da misalin ƙarfe 6:30 na safiyar Lahadi a lokacin da yake tafiya bakin aikinsa.
Rahotanni na cewa ‘yan sanda da ‘yan banga na kan hanyarsu ta zuwa kama masu garkuwa da mutane. A cewar wani ganau, kwatsam masu garkuwar sun fito daga cikin daji inda suka buɗe wuta kan wata motar Bas ta kasuwanci da nufin yin garkuwa da su.
KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun kashe ‘yan bindiga biyu a Zamfara
Daga karshe dai babu ɗaya daga cikin fasinjojin da aka sace amma jami’in TRACE ya yi rashin sa’a.
Da aka tuntuɓi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Abeokuta, inda ya ce tuni rundunar da ke yaƙi da masu garkuwa da mutane a jihar ta bi sahun masu garkuwa da mutane.
“Rundunar mu na yaƙi da garkuwa da mutane tuni ta bi su, muna tafe dazuzzuka kuma mun san za a kama su duka.
“Jihar Ogun ba wurin da masu laifi za su sasanta ba. Ko dai su fita ne ko kuma mu fitar da su daga wannan jihar,” inji shi.
[…] KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da jami’in kula da zirga-zirgar ababen hawa a Ogun […]