An kori ‘yan sandan dake tsaron Rarara saboda wasa da alburusai

1
403

Hukumar ‘yan sandan Najeriya, a ranar Alhamis, ta kori jami’an da ke tsaron fitaccen mawaƙin siyasar nan na jam’iyar APC mai mulki, Dauda Adamu Kahutu Rarara.

Olumuyiwa Adejobi, kakakin rundunar ‘yan sandan, wanda ya sanar da matakin a hedikwatar rundunar da ke Abuja, ya ce an kori jami’an ne saboda ɓatar da harsasai babu gaira babu dalili.

A baya-bayan nan dai an kama masu tsaron mawaƙin suna harba harsasai a sama yayin da mawaƙin ya shiga motarsa ​​a Kano, inda yake zaune.

Matakin nasu ya haifar da ɓacin rai kuma rundunar ta sha alwashin ɗaukar mataki. A wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, Adejob ya ce, “Bayan koke-koke da bincike kan shaidun bidiyo da aka yi ta yaɗa wa a ranar Juma’a 7 ga Afrilu, 2023, a kafafen sada zumunta na yanar gizo na cin hanci da rashawa, da rashin ɗa’a, da kuma yin amfani da makamai ba bisa ƙa’ida ba a kan wasu ‘yan sanda daga Sashen Kariya na Musamman (SPU).

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun kama jami’an tsaron Rarara saboda harbin iska

Base 1, Kano, da kuma zaman shari’ar da aka yi a kan ‘yan sandan da abin ya shafa da rundunar ‘yan sanda ta ‘Force Provost Marshal’ ta kori jami’ai uku daga SPU Base 1 Kano, bisa laifukan cin mutunci da amfani da bindigogi, da amfani da ƙarfin iko, rashin tarbiyya, da almubazzaranci da alburusai.

“Masu tsaron Rararan su uku, Isfekta Ɗahiru Shuaibu, Sajen Abdullahi Badamasi, da Sajen Isah Ɗanladi sun kasance tare da mawaƙin a Kano suna yi masa aikin rakiya.

A yayin gudanar da aikinsu a ranar Juma’a 7 ga Afrilu, 2023 a ƙauyen Kahutu, jihar Katsina, jami’an sun yi ta harbin bindiga daga bindigu zuwa sama duk da manufofin ‘yan sanda na hana harbe-harbe a iska, tsarin aiki da kuma umarnin rundunar da abin ya shafa; da kuma yin watsi da yiwuwar taron jama’a a wurin wanda ya haɗa da ƙananan yara.

Wannan aika-aika ba kawai laifi ba ne da rashin ɗa’a amma kuma abin kunya ne ga rundunar ta ƙasa baki ɗaya.

“Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta na yiwa dukkan jami’an diflomasiyya da su tabbatar sun gudanar da ayyukansu kamar yadda doka ta tanada domin kaucewa saɓawa tanade-tanaden ta da kuma sanya wa jami’anta takunkumi.

1 COMMENT

Leave a Reply