Al’ummar Yobe sun koka da rashin kula da hukumomin ba da agaji

0
375

Daga Najibullah Adamu

Mazauna yankin Gujba ta gabas, al’ummar jihar Yobe da ta ƙunshi gundumomin siyasa guda biyar da suka haɗa da Goniri, Gotala/Gotumba, Daɗingel, Ngurbuwa da kuma Mandunari sun koka da yadda hukumomin agaji ke yi musu sakaci a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda rikicin Boko Haram ya shafa.

Ƙungiyar ci gaban matasa ta Gujba ta Gabas ta yi wannan koke a cikin wata takardar manema labarai da Daraktan yaɗa labarai na ƙungiyar Kwamared Lawan Mustapha ya raba wa wakilinmu a ranar Alhamis.

KU KUMA KARANTA: An yi kira ga hukumar Lantarki ta YEDC ta inganta yadda take ba da wuta a Yobe

A cewarsa, al’ummar yankin na ɗaya daga cikin wuraren da tashe-tashen hankula suka fi shafa a jihar inda ya nuna cewa a shekarar 2015 akasarin mazauna yankin sun ƙauracewa gidajensu tare da yin hijira zuwa wurare daban-daban a ƙasar.

“A halin yanzu al’ummomi huɗu sun dawo tun a shekarar 2017 sun bar ɗaya wato Mandunari, tun bayan dawowar mutanen yankin ba su da cikakkiyar damar shiga gonakinsu, saboda ana ganin ragowar ‘yan tayar da ƙayar bayan nan, a da can kuma saboda takunkumin da sojoji suka yi.

“Hakan ya sa mutanen yankin ba su iya noma abin da za su ci har na tsawon watanni shida ba a cika shekara ba, lamarin da ya jefa da dama cikin mawuyacin hali.

“Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Yobe (YOBSEMA) ta mayar da yankin gefe. “A cikin shekarun da suka gabata, SEMA ta raba abinci da kayan abinci da yawa a jihar amma abin takaici shi ne, yankin bai amfana da kasancewa mafi rauni ba.

“Kwanan nan, SEMA ta raba kayayyakin abincin watan Azumi sama da 2000 wanda sarki Salman ya ɗauki nauyinsa amma abin takaici, babu wani daga cikin al’ummomin huɗu da aka bawa, babu mutum ko ɗaya da suka bawa, babu wanda ya amfana duk da cewa su ne suka cancanci taimakon”. Ya yi zargin.

Leave a Reply