Buhari, Tinubu sun miƙa ta’aziyyar rasuwar matar Aminu Ɗantata

2
266

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu sun bayyana alhininsu dangane da rasuwar Hajiya Rabi Ɗantata, matar hamshaƙin ɗan kasuwar nan, mai taimakon jama’a kuma uban gidan Ɗantata na Kano, Alhaji Aminu Ɗantata.

Shugaban, a cikin saƙon ta’aziyyar da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Garba Shehu, ya fitar ranar Lahadi a Abuja, ya ce za a tuna da marigayiyar bisa tausayawa da taimakon da ta ke yiwa al’umma.

“Tana da sha’awar hidima ga mutane. Ta kasance mai farin jini mai son raba duk abin da take da shi. “Rayuwarta mai sauƙi ce, ga ta da tausayi ta kasance abin ƙarfafawa ga duk waɗanda ke kewaye da ita,” in ji shi.

KU KUMA KARANTA: Matar gwamnan Kano na farko, Ladi Bako ta rasu

Ya kuma yi addu’ar Allah ya karɓi ayyukanta na alheri, ya kuma baiwa iyalan Ɗantata ikon jure wannan babban rashi.

Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar, a cikin saƙon ta’aziyyar da mai magana da yawunsa Abdulaziz Abdulaziz ya sanya wa hannu a safiyar Lahadi, ya bayyana rashin lafiyar a matsayin wani labari mai ban tausayi da ya wuce danginta da kuma al’ummarta.

“Rashin mace mai kima kamar Hajiya Rabi, rashi ne da ya shafi dukkan al’umma ba wai dangi da iyalinsu kawai ba.

“Har ila yau, ta kasance macen da ta tsaya tare da mijinta a ko’ina, inda take taimaka masa wajen renon yara masu nagarta da suka rungumi sananniyar hanyar kasuwanci da masana’antu na dangin Ɗantata.

“Ina baƙin ciki tare da ta’aziyya ga Alhaji Aminu Ɗantata na wannan rashin da aka yi tare da Alhaji Tajudeen Ɗantata da sauran ‘ya’yanta da ‘yan’uwanta kan wannan rashin da ba za a iya misalta shi ba. Dole ne in kuma yi ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar Jihar Kano,” inji shi.

Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya yi addu’ar Allah ya jiƙan marigayiyar, ya kuma baiwa iyalanta hakurin jure rashin.

2 COMMENTS

Leave a Reply