Gwamna Zulum ya ƙaddamar da aikin gina gadar sama ta biyu a Borno

2
358

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya ƙaddamar da aikin gina gadar sama ta biyu a birnin Maiduguri domin ƙara rage cunkoso da kuma ƙara samar da ababen more rayuwa a babban birnin jihar.

Zulum ya gina gadar sama ta farko a Maiduguri ta sama da ƙasa. An gudanar da aikin ne a kewayen layin kwastam tare da hanyoyi zuwa sassa uku na cikin garin. An fara shi a watan Janairun shekarar 2020 kuma Shugaba Buhari ne ya ƙaddamar da shi a watan Disamba 2021.

Gadar sama ta biyu kuma za a yi ta ne a kusa da babban titin Borno Express wanda ke da hanyar T-junction da hanyoyin da suka haɗa muhimman sassa uku na Maiduguri zuwa filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa, filin wasa na garin da Tashan Kano, da kuma tsakiyar birnin (Secretariat, Post Office, Monday market da sauransu).

Gadar saman za ta yi tsayin kusan mita 600 na gadar siminti tare da ƙarin hanyoyin sadarwa. Da yake jawabi a wajen taron, Zulum ya ce, “Insha Allahu, mu (Gwamnatin Jihar Borno) za mu tabbatar da sakin kuɗaɗen kamar yadda ya kamata. Ina roƙon ku (‘yan kwangila) da ku tabbatar an yi aiki mai inganci.

KU KUMA KARANTA: Mace ɗaya ‘tilo’ mai gyaran wayar salula a jihar Borno

“Insha Allahu a mataki na gaba na rayuwarmu za mu samar da ƙarin rabon dimokuradiyya ga mutanen Borno.” Wani kamfanin ƙasar China, Kamfanin Injiniya (EEC) ne ya samu kwangilar gadar sama ta biyu a Borno kan kuɗi Naira biliyan 5.8. Kamfanin ya samu nasara ne bayan wani tsari na neman takara biyo bayan takardun da aka yi a hedikwatar ma’aikatar ayyuka ta jihar da ke Maiduguri.

Kwamishinan Ayyuka na Borno, Architect Isa Garba Haladu, ya rattaɓa hannu kan yarjejeniyar kwangila a madadin gwamnatin jihar Borno yayin da wakilin EEC ya rattaɓa hannu a kan kamfanin kasar Sin. Ana sa ka ran za a kammala aikin kafin ƙarshen wannan shekara, 2023, ba tare da kowane ƙalubale.

2 COMMENTS

Leave a Reply