Kotu ta umarci wani magidanci da ya yanka zakaransa, saboda ya taƙura wa makwabta

1
239

Kotu ta umarci wani magidanci ɗan Kano da ya yanka zakaransa saboda ya taƙura makwaftan da cara.

Wata kotun Majistiri da ke Kano ta umarci wani Isyaku Shu’aibu da ke da babban zakara mai cara, da ya yanka shi. Makwaftan wadanda suka shigar da kara a gaban Kotun, su biyu ne, inda suka ce caran Zakaran yana hana su barci da kwanciyar hankali a unguwar.

A wani hukunci da kotun ta yanke a ranar Talata, 4 ga Afrilu, Alkaliyar kotun Halima Wali ta ba wa Shu’aibu umarnin yanka Zakaran nasa a ranar Juma’a 7 ga Afrilu, 2023.

KU KUMA KARANTA: An kori ɗan jarida saboda sukar gwamnatin Borno

Ɗaya daga cikin waɗanda suka shigar da karar, Yusuf Mohammed, na unguwar Ja’en, ya shaida wa kotun cewa Zakaran yana damunsu da kuka sosai (cara), yana tauye musu hakkinsu na yin barci mai dadi.

Shu’aibu, wanda ya yarda cewa Zakaran na da basirar yin ihu, ya roki kotu da ta ɗage hukuncin har sai ranar Juma’a. Alkalin kotun, wanda ya gamsu da hujjar masu korafin, ya yanke hukuncin cewa za a kama Zakara a yanka shi a ranar 7 ga Afrilu.

A halin da ake ciki kuma, wata kotun majistiri da ke Enugu ta bayar da diyyar Naira 150,000 ga wani mutum da ya shigar da kara a gaban wata matar da ta karya wata yarjejeniya.

Matar dai ta karɓi Naira 3,000 daga gare shi a matsayin kuɗin safara da nufin za ta ziyarce shi, amma ta kasa zuwa. Daga nan ne ya kai ta kotu saboda ta samu kuɗi bisa zargin karya, kuma Alkalin kotun ya umarce ta da ta biya shi dubu dari da Hamsin (N150,000).

Mai shigar da ƙara ta shaida wa kotun cewa bayan ya aika mata da kuɗin ne ta kashe wayarta.

Lauyan da aka fi sani da Egi Nupe ne ya bayyana lamarin a shafinsa na Twitter mai suna @egi-nupe, inda ya ce Alkalin kotun ya bayar da diyya ga matar ne domin ya zama abin hanawa.

1 COMMENT

Leave a Reply