Yadda fusatattun matasa suka ƙone mutum biyar da ake zargin ɓarayi ne masu amfani da babur na adaidaita

Wasu fusatattun matasa a ranar Asabar ɗin da ta gabata sun bankawa wasu mutane biyar da ake zargin ‘yan fashi ne wuta a yankin Nkpor da ke kusa da Onitsha a jihar Anambra.

An tattaro cewa an ƙona waɗanda ake zargin ‘yan fashi ne bayan da suka gaza a yunkurinsu na kwace wayar tarho daga masu wucewa a yankin.

Wani ganau ya shaida cewa waɗanda ake zargin kan yi amfani da babur mai ƙafa uku ne wajen yi wa jama’a fashin wayoyinsu, jakunkuna, kuɗi da sauran kayayyaki masu daraja a yankin.

Majiyar wadda ba ta so a buga sunansa ba saboda dalilai na tsaro, ta ce, “A ‘yan kwanakin da suka gabata waɗanda ake zargin sun addabar jama’a.

“Sun yi amfani da babur na adaidaita (Babur mai ƙafa uku) suna wa mutane fashin kayansu bayan sun gudu amma suka yi rashin sa’a yayin da wasu fusatattun matasa suka kama su inda suka banka musu wuta a lokacin da suke ƙoƙarin yi wa wasu masu wucewa fashin wayoyinsu.”

KU KUMA KARANTA: Yadda ‘yan sanda suka kama matashin da ake zargi da kai hari kan ayarin motocin matar gwamna

Wani faifan bidiyo daga wurin ya nuna lokacin da ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin ke ci gaba da motsi yayin da wutar ke kona inda jama’a suka ke waye shi, suna jifansa da wasu abubuwa, yayin da abokan aikinsa kuma ke cigaba da ci da wuta.

Da aka tuntubi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Anambra a ranar Lahadi, DSP Tochukwu Ikenga, ya yi Allah-wadai da wannan aika-aika, ya kuma buƙaci jama’a da su rinƙa kai waɗanda ake zargi zuwa ofishin ‘yan sanda a duk lokacin da aka kama su domin hakan zai taimaka wa jami’an tsaro.

Ikenga, ya ce an kwato wayoyin hannu guda biyar na nau’ukan iri daban-daban da kuma babur uku da ake zargin wadanda ake zargin sun sace daga wurin da lamarin ya faru.

Ya ce, “Kafin ‘yan sanda su isa wurin da misalin karfe 5:30 na yamma, tuni an ƙona waɗanda ake zargin.

Jami’anmu sun ƙwato wayoyi biyar iri daban-daban da kuma babur uku da ake zargin waɗanda ake zargin sun yi awon gaba da su ne.

“A halin da ake ciki, rundunar ta yi Allah-wadai da wannan aika-aika gaba ɗaya, kuma a kodayaushe tana ƙarfafa gwiwar jama’a da su kai waɗanda ake zargi zuwa ofishin ‘yan sanda a duk lokacin da aka kama su.

Hakan zai taimaka wa ‘yan sanda wajen gudanar da bincike mai inganci kan ayyukan waɗanda ake zargin tare da gurfanar da su a gaban kuliya bisa manyan dokoki.” In ji shi.


Comments

One response to “Yadda fusatattun matasa suka ƙone mutum biyar da ake zargin ɓarayi ne masu amfani da babur na adaidaita”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Yadda fusatattun matasa suka ƙone mutum biyar da ake zargin ɓarayi ne masu amfani da babur na adai… […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *