Aƙalla mutane 25 ne suka mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a Udubo kan hanyar Hadeja-Potiskum a ƙaramar hukumar Gamawa a jihar Bauchi.
Wasu mutum 10 ne aka ruwaito sun samu raunuka daban-daban a hatsarin ɗaya tilo da ya rutsa da wata motar bas ƙirar Toyota Hummer.
Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta tarayya reshen jihar Bauchi Yusuf Abdullahi ne ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Juma’a.
Ya ce mutane 35 ne da suka haɗa da manya maza 19, manya mata 11, yara maza biyu da mata uku hatsarin ya rutsa da su.
KU KUMA KARANTA: Wata mace ta mutu lokacin da jirgin ƙasa ya murkushe mota a Abuja
A cewarsa, direban motar bas din ya rasa yadda zai yi, inda ya ci karo da mutane 11 da suke fakewa a karkashin wata bishiya da ke kusa da wurin wankin mota.
Abdullahi ya ce, “Eh, an samu hatsarin mota ɗaya tilo a Udubo, daura da hanyar Haɗeja-Potiskum a ƙaramar hukumar Gamawa ta jihar Bauchi.
Hatsarin ya faru ne a ranar Alhamis, 23 ga watan Maris, 2023. “Hatsarin ya shafi wata motar bas Toyota Hummer mai launin toka mai lamba JMA 59XA.
Hatsarin dai ya faru ne sakamakon gudun wuce gona da iri wanda ya yi sanadiyar fashewar taya tare da rasa yadda za a iya sarrafa motar.
“Direban wanda har yanzu ba a san sunansa ba, ya rasa yadda zai yi, inda ya ci karo da wasu mutane da suke fakewa a ƙarkashin wata bishiya, saboda yanayin zafi, suna ƙarƙashin bishiyar suna shan inuwa kuma an kashe wasu daga cikinsu.
“Mutane 24 ne ke cikin motar Hummer, yayin da sauran mutane 11 da ke fakewa a ƙarƙashin bishiyar da ke kusa da wurin wanke mota kamar yadda rundunar ‘yan sandan Najeriya ta bayyana.”
“A asibitin ne wani likita ya tabbatar da mutuwar mutane 25 – manya maza tara, manya mata 11, yara maza biyu da mata uku. Wasu 10 sun sami raunuka daban-daban. “
A halin da ake ciki kuma, shugaban hukumar kiyaye hadurra ta FRSC, Mista Dauda Biu, ya bayar da umarnin kafa kwamanda tare da cibiyoyin hukumar a garin Gamawa da ke jihar Bauchi, domin daƙile hadurran mota.
Jami’in kula da ilimin jama’a na tare da huɗɗa da jama’a na hukumar, Bisi Kazeem, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce Biu ya bayar da wannan umarni ne a Abuja sakamakon mummunan hatsarin da ya faru a jihar ta Bauchi.
Ya ce ya zama dole a kafa dokar da za ta magance matsalolin da suka shafi cin zarafi da kuma yin amfani da tsaro a wannan hanya domin daƙile wuce gona da iri na direbobin da ke yin kuskure.