Shahararren ɗan jarida ya mutu yayin tattaki zuwa ofis saboda karancin takardun kuɗi

0
469

Wani fitaccen mai gabatar da shirye-shirye a gidan rediyo mai zaman kansa da ke Ibadan, Fresh FM Nigeria, wanda aka fi sani da Baba Bintin ya rasu a kan hanyarsa ta zuwa gidan rediyon domin shirinsa na safiyar Asabar.

An bayyana rasuwar Baba Bintin ne a wani shirin gidan rediyo da tagwayen gidan rediyon, Komolafe Olaiya da Olalomi Amole, Oyin Ado suka gabatar a ranar Asabar.

Tun da farko a cikin shirin na safiyar ranar Asabar, ’yan biyu sun yi bayani ne kan rashin jinkirin da mai gabatar da shirin ya yi biyo bayan rashin halartarsa gidan radiyon da wuri, amma a ƙarshen shirin, masu gabatar da shirye-shiryen sun sanar da cewa ya rasu ne a lokacin da yake tattaki daga unguwar Amuloko zuwa Fresh FM a safiyar yau (Asabar) inda yayi fatan samun kuɗi daga masu POS.

KU KUMA KARANTA: Yadda mace mai ciki ta mutu a asibitin Kano sakamakon rashin takardun kuɗi

A cikin wani faifan murya da aka kunna a gidan rediyon, wani mutum ya ce sun same shi a kwance a hanyarsa ta zuwa ofis, suka garzaya da shi asibitin Kwalejin Jami’ar Ibadan, UCH, amma ya mutu da isarsu asibiti.

Baba Bintin wanda yakan yi yaren Ijesha kuma wanda Komolafe ke yi wa laƙabi da “Boda Olu” da “Uncle” ya kasance mai gabatar da shirin barkwanci a shirin Oyin Ado a ranar Asabar a gidan rediyo don bayar da bayanai kan kasuwannin jihar.

Leave a Reply